Hadisai

Kada ɗayanku ya ce: Ya Allah Ka gafarta mini in Ka so, Ka yi mini rahama in Ka so, Ka azirtani in Ka so, ya ƙudirce niyyar rokonsa, lallai Shi Yana aikata abinda Yake so, babu mai tilasta Shi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَن أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «لاَ يَقُلْ أَحَدُكُمْ: اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي إِنْ شِئْتَ، ارْحَمْنِي إِنْ شِئْتَ، ارْزُقْنِي إِنْ شِئْتَ، وَليَعْزِمْ مَسْأَلَتَهُ، إِنَّهُ يَفْعَلُ مَا يَشَاءُ، لاَ مُكْرِهَ لَهُ». ولمسلم: «وَلَكِنْ لِيَعْزِمِ الْمَسْأَلَةَ وَلْيُعَظِّمِ الرَّغْبَةَ، فَإِنَّ اللهَ لَا يَتَعَاظَمُهُ شَيْءٌ أَعْطَاهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ɗayanku ya ce: Ya Allah Ka gafarta mini in Ka so, Ka yi mini rahama in Ka so, Ka azirtani in Ka so, ya ƙudirce niyyar rokonsa, lallai Shi Yana aikata abinda Yake so, babu mai tilasta Shi". Kuma riwayar Muslim: "Sai dai ya ƙudirce niyyar tambaya kuma ya girmama kwaɗayi, domin Allah wani abu da Ya bada shi ba ya yi maSa girma".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga rataya addu'a da wani abu koda ya kasance da Mashi'ar Allah ne (ganin damar Allah) domin hakan wani al'amari ne abin sani abin sakankancewa cewa shi ba'a gafartawa sai idan tsarki ya tabbatar maSa Ya so, kuma babu wata ma'ana ga sharɗanta Mashi'a; domin cewa ita kaɗai ana sharɗantata ne ga wanda ya inganta daga gare shi ya yi aiki ba tare da ya so ba da tilastawa da waninsa daga abinda Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya tsarkaka daga gare shi, haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana a cikin ƙarshen hadisin da faɗinSa lallai shi Allah babu mai tilasta shi, kamar yadda cewa Allah babu wani abu daya da ya bada shi yake girmama a gareShi, kuma Shi ba mai gajiyawa bane kuma wani abu ba ya girmama a gareShi har ace: Idan Ka so, kuma rataya shi da Mashi'a wani nau'i ne na wadatuwa daga gafararSa, to faɗin mai faɗa: Idan Ka so Ka bani kaza to Ka aikata, ba'ayin amfani da wannan sai tare da wanda ya wadata daga gare shi, ko tare da wanda ya gajiya, amma tare da mai iko kuma tare da mai buƙatuwa gare shi to cewa shi ya ƙudirce niyyar roƙonsa, kuma ya yi roƙo irin roƙon mabuƙaci mai tsananin buƙatuwa zuwa ga abinda ya roƙe shi, kuma ya fake zuwa ga Allah; domin cewa Shi Mawadaci ne cikakke, Mai iko a kan dukkan komai.

Fa'idoji

  • Hani daga rataya addu'a da Mashi'a (ganin dama).
  • Tsarkake Allah daga abinda ba ya dacewa da Shi, da yalwar falalarSa, da cikar wadatuwarSa, da karamcinSa da kyautarSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
  • Tabbatar da kamala ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
  • Girmama kwaɗayi ga abinda ke gurin Allah da kyautata zato gare Shi - tsarki ya tabbatar maSa -.
  • Rataya addu'a da Mashi'a (ganin dama) yana faruwa daga wasu daga cikin mutane alhali su ba su sani ba, misali faɗin: Allah Ya yi maka sakayya da alheri in Allah Ya so, Allah Ya yi masa rahama in Allah Ya so, to wannan ba ya halatta saboda hadisin babin.
Sharhi: العربية

نَهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن تَعْلِيْق الدعاء بشيء حتى لو كان بمشيئة الله؛ فإن ذلك أمر معلوم مُتَيَقَّن أنه لا يغفر إلا أن يشاء سبحانه، ولا معنى لاشتراط المشيئة؛ لأنها إنما تشترط فيمن يصح منه أن يفعل دون أن يشاء بالإكراه وغيره مما تنزه الله سبحانه عنه، وقد بين ذلك صلى الله عليه وسلم في آخر الحديث بقوله فإنه لا مُكْرِه له، كما أن الله لا يَتَعَاظَمُه شيء أعطاه وليس بعاجز ولا يكبُر عليه شيء حتى يقال: إن شئت، وتعليقه بالمشيئة نوع من الاستغناء عن مغفرته، فقول القائل: إن شئت أن تعطيني كذا فافعل، لا يستعمل هذا إلا مع الغنى عنه أو مع العاجز، وأما مع القادر ومع الاضطرار إليه والحاجة إليه فإنه يَعزم مسألته، ويَسأل سؤال فقير مضطر إلى ما سأله، ويلجأ إلى الله؛ لأنه الغني الكامل، القادر على كل شيء.

  • النهي عن تعليق الدعاء بالمشيئة.
  • تنزيه الله عما لا يليق به، وسعة فضله، وكمال غناه، وكرمه وجوده سبحانه وتعالى.
  • إثبات الكمال لله عز وجل.
  • تعظيم الرغبة فيما عند الله وحسن الظن به سبحانه.
  • يقع من بعض الناس تعليق الدعاء بالمشيئة وهم لا يشعرون، مثل قول: جزاك الله خيرًا إن شاء الله، الله يرحمه إن شاء الله، فهذا لا يجوز لحديث الباب.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari