Hadisai

Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad

Rubutun Larabci

عن ابن عباس رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «من اقتبَسَ علْمًا مِنَ النُّجُومِ اقْتبَسَ شُعبَة مِن السِّحرِ، زادَ ما زادَ».

Fassara

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara".

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana duk wanda ya koyi, ya samu wani tsagi na ilimin taurari da buruji da kuma kafa dalili da motsinsu da shigarsu da fitarsu a kan abin da zai faru a bayan ƙasa na mutuwar wane, ko rayuwarsa, ko rashin lafiyarsa, da makamancin haka cikin abinda zai faru nan gaba, to, haƙiƙa ya koyi wani tsagi na sihiri, kuma duk lokacin da mutum ya ƙara wannan ilimin, to, ya ƙara asiri [tsafi] ne.

Fa'idoji

  • Haramcin ilimin taurari wanda yake na ba da labarin abin da zai faru nan gaba, dogaro da yanayin taurari, domin yana cikin iƙirarin sanin gaibu.
  • Ilimin taurari haramun ne, yana cikin nau’ukan asiri [tsafi] wanda yake kore Tauhidi, saɓanin nazarin taurari domin sanin inda mutum ya nufa, ko sanin alƙibla, ko sanin shigar lokacin wasu bukukuwa, ko watanni, to, wannan ya halatta.
  • Duk lokacin da ya ƙara a koyar ilimin taurari, to, yana ƙara koyar wani kaso ne na asiri [tsafi].
  • Taurari suna da fa'idoji uku, Allah ya ambace su a LittafinSa: Ƙawa ga sama, alamomi da za’a dinga ganewa da su, jifa ga shaiɗanu.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن تَعَلَّم وأَخَذَ من علم النجوم والأبراج والاستدلال بحركاتها ودخولها وخروجها على الحوادث الأرضية من موت فلان أو حياته أو مرضه، ونحو ذلك مما سيقع في المستقبل، فقد تَعَلَّمَ جزءًا من السحر، وأنه كلَّما أكثر الإنسان هذا العلم فقد أكثر من السحر.

  • تحريم التنجيم الذي هو الإخبار عن المستقبل اعتمادًا على أحوال النجوم؛ لأنه من ادعاء علم الغيب.
  • أن التنجيم المُحَرَّم من أنواع السحر المنافي للتوحيد، بخلاف النظر في النجوم لمعرفة الاتجاهات أو القِبْلة أو دخول المواسم والشهور فهو مباح.
  • كلما زاد في تَعَلُّمِه للتنجيم فهو يزيد من تَعَلُّمِ شُعَبِ السحر.
  • للنجوم ثلاث فوائد ذكرها الله في كتابه: زينة للسماء، وعلامات يهتدى بها، ورجوم للشياطين.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari