Hadisai

Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَحْسَنَ النَّاسِ خُلُقًا.

Fassara

Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u.

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa cikar kyawawan ɗabi’u, yana da wannan rigayar a dukkanin kyawawan ɗabi’u, kamar kyakkyawar magana, bayar da kyauta, sakin fuska, rashin cutarwa, juriyarsa ga mutane.

Fa'idoji

  • Cikar ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
  • Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne babban abin koyi a kyawawan ɗabi’u.
  • Kwaɗaitarwa a kan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kyawawan ɗabi’u.
Sharhi: العربية

كان النبيُّ صلى الله عليه وسلم أكملَ الناس خُلُقًا، وله السَّبْقُ في جميع الأخلاق والمحاسن، من طِيْبِ الكلام، وبذلِ الخير، وطَلَاقة الوجه، وكَفِّ الأذى واحتمالِهِ من الآخرين.

  • كمال خُلق النبي صلى الله عليه وسلم.
  • النبي صلى الله عليه وسلم هو القدوة الكاملة في حسن الخُلُق.
  • الحث على التأسي بالنبي صلى الله عليه وسلم في حسن خُلُقه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari