Hadisai

Babu wani mutum da zai yi mini sallama har sai Allah Ya dawo mini da raina har sai na mayar masa da sallamar

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Sanadinsa Hasan neAbu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلَّى الله عليه وسلم قال: «ما مِنْ أحَدٍ يُسلِّمُ علي إلا ردَّ اللهُ عليَّ رُوحي حتى أردَّ عليه السَّلامَ».

Fassara

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Babu wani mutum da zai yi mini sallama har sai Allah Ya dawo mini da raina har sai na mayar masa da sallamar".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa shi ana dawo masa da ransa dan ya amsa sallama ga dukkan wanda ya yi masa sallama , daidai ne ya kasance a kusa yake ko a nesa; rayuwar barzahu da ƙabarbura wani al'amari ne na gaibu, babu wanda ya san haƙiƙaninsu sai Allah, Shi Mai iko ne akan dukkan komai.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa akan yawaita salati da sallama ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  • Rayuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin ƙabarinsa ita ce mafi cikar rayuwar da mutum zai rayu a cikin barzahunsa, babu wanda ya san haƙiƙaninta sai Allah - Maɗaukakin sarki -.
  • Hadisin babu wata hujja a cikinsa ga wanda yake faɗin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rayuwa kamar yadda muke rayuwa, har ma'abota shirka suke kafa hujja da shi akan neman agaji da shi - tsira da amincin su tabbata agare shi -, kawai ita rayuwa ce ta barzahu.
Sharhi: العربية

يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنّه تُرَدُّ إليه رُوحُه ليَرُدَّ السلامَ على كل مَن سلَّم عليه سواء كان قريبًا أو بعيدًا؛ وحياة البَرْزَخ والقبور أمرٌ غيبي، لا يَعلم حقيقتَها إلا الله، وهو على كل شيء قدير.

  • الحث على الإكثار من الصلاة والسلام على النبي صلى الله عليه وسلم.
  • حياة النبي صلى الله عليه وسلم في قبره هي أكملُ حياة يحياها إنسان في بَرْزَخِه، فلا يَعلم حقيقتها إلا الله تعالى.
  • الحديث ليس فيه حُجّة لمن يقول بحياة رسول الله صلى الله عليه وسلم حياةً كما نعيشها نحن، حتى لا يَستدِلّ به أهل الشرك على الاستغاثة به عليه الصلاة والسلام، وإنما هي حياة برزخية.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari