Hadisai

‌Wanda ya nemi sanin wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da shi ba ya nemansa sai dan ya samu wata haja ta duniya da shi ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙima

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ تَعَلَّمَ عِلْمًا مِمَّا يُبْتَغَى بِهِ وَجْهُ اللَّهِ عَزَّ وَجَلَّ لَا يَتَعَلَّمُهُ إِلَّا لِيُصِيبَ بِهِ عَرَضًا مِنَ الدُّنْيَا لَمْ يَجِدْ عَرْفَ الْجَنَّةِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ» يَعْنِي رِيحَهَا.

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Wanda ya nemi sanin wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da shi ba ya nemansa sai dan ya samu wata haja ta duniya da shi ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙima» wato ƙanshinta.

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya nemi sanin ilimin shari'a wanda asali a cikinsa shi ne a nufi yardar Allah - Maɗaukakin sarki - da shi ba ya nemansa ba ne kawai sai dan ya samu wani rabo da wani jin daɗi na duniya da shi na dukiya ko alfarma to ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙiyama.

Fa'idoji

  • Wajabcin ikhlasi a cikin neman ilimi, da kuma kwaɗaitarwa akan hakan.
  • Gargaɗarwa mai tsanani daga riƙo da ilimin shari'a saboda riya ko abin neman duniya, kuma cewa hakan yana daga cikin manyan zunubai.
  • Cewa wanda ya nemi ilimi saboda Allah - Maɗaukakin sarki - sai duniya ta zo masa dan bi to ya halatta ya karɓeta, hakan ba zai cutar da shi ba.
  • Sindi ya ce: Faɗinsa (ƙanshin aljanna): ƙanshi, kai matuƙa ne a cikin haramta aljanna; domin cewa duk wanda ba zai ji ƙanshin abu ba to ba zai same shi ba.
  • Wanda ya koyi wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah da shi saboda neman aiki, ko saboda wasu buƙatu na duniya daban; to wajibi ne ya tuba zuwa ga Allah daga hakan, Allah zai goge masa abinda ya faru na gurɓatacciyar niyya kuma Shi Ma'abocin falala ne Mai girma - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
  • Wannan gargaɗarwar ga mai neman ilimin shari'a ne, amma wanda ya nemi wani ilimi daga cikin ilimummukan duniya saboda jin daɗin duniya kamar Injiniyarin ko Kimiyya da wasunsu saboda duniya to shi niyyarsa ta tabbata gare shi.
Sharhi: العربية

بيَّن النبي صلى الله عليه وسلم أنَ من تعلم العلم الشرعي الذي الأصل فيه أن يراد به رضى الله تعالى لا يتعلمه إلا ليصيب وينال به حظًا ومتاعًا من الدنيا من مالٍ أو جاهٍ لم يجد ريح الجنة يوم القيامة.

  • وجوب الإخلاص في طلب العلم، والحث على ذلك.
  • التحذير الشديد من اتخاذ العلم الشرعي رياءً أو مطية للدنيا، وأن ذلك من كبائر الذنوب.
  • أن من طلب العلم لله تعالى وجاءته الدنيا تبعا جاز له أخذها، ولم يضره ذلك.
  • قال السندي: قوله (عرف الجنة): الرائحة، مبالغة في تحريم الجنة؛ لأن من لا يجد ريح الشيء لا يتناوله.
  • من تعلم علمًا مما يبتغى به وجه الله من أجل الوظيفة، أو من أجل أغراض أخرى؛ فإن عليه التوبة إلى الله من ذلك، والله يمحو عنه ما حصل من النية الفاسدة وهو ذو الفضل العظيم سبحانه وتعالى.
  • هذا التحذير لطالب العلم الشرعي، أما من طلب علمًا من علوم الدنيا لأجل متاع الدنيا كالهندسة والكيمياء وغيرهما لأجل الدنيا فله نيته.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari