Hadisai

Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن عثمان بن عفان رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ تَوَضَّأَ فَأَحْسَنَ الْوُضُوءَ خَرَجَتْ خَطَايَاهُ مِنْ جَسَدِهِ حَتَّى تَخْرُجَ مِنْ تَحْتِ أَظْفَارِهِ».

Fassara

Daga Usaman Bn Affan -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa".

Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabba a gare shi yana ba da labari cewa wanda ya yi alwala tare da kula da sunnonita da ladubbanta, to, hakan zai kasance daga sababi na kankare laifuka, da share kukurai, har sai zunubansa sun fita ta ƙarƙashin farcensa na hannu da ƙafa.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa a kan koyan alwala da sunnonita da kuma ladubbanta, kana da aiki da hakan.
  • Falalar alwala, kuma tana kankare zunubai ƙanana, amma manya sai an musu tuba.
  • Sharaɗin fitar laifukan shi ne cika alwalar, da kuma yinta ba tare da kurakurai ba, kamar dai yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana.
  • Kankare zububai a wannan Hadisin an ƙayyadeshi ne da nisantar manyan laifuka, da kuma tuba daga su, Allah maɗaukaki ya ce: Idan kuka nisanci manyan abubuwan da ake hanaku, to, zamu kankare muku laifukanku.
Sharhi: العربية

يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن توضَّأ مع مُراعاةِ سُننِ الوضوء وآدابِه، كان ذلك من أسبابِ تكفيرِ السيئات وحَطِّ الخطايا، «حتى تخرج» ذنوبُه من تحت أظفار يديه ورجليه.

  • الحث على الاعتناء بتعلُّم الوضوء وسننه وآدابه، والعمل بذلك.
  • فضل الوضوء، وأنه كفارة للذنوب الصغائر، أما الكبائر فلا بد من التوبة.
  • شرط خروج الخطايا هو إكمال الوضوء والإتيان به بدون إخلال كما بينه النبي -صلى الله عليه وسلم-.
  • تكفير الذنوب في هذا الحديث مُقيَّدٌ باجتناب الكبائر والتوبة منها، قال تعالى: (إِنْ تَجْتَنِبُوا كَبَائِرَ مَا تُنْهَوْنَ عَنْهُ نُكَفِّرْ عَنْكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ) [النساء:31].

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari