Hadisai

Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي الدرداء رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ حَفِظَ عَشْرَ آيَاتٍ مِنْ أَوَّلِ سُورَةِ الكَهْفِ، عُصِمَ مِنَ الدَّجَّالِ». وفي رواية: «مِنْ آخِرِ سُورَةِ الكَهْف».

Fassara

Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya haddace ayoyi goma a zahirin zuciya (hadda) daga farkon Suratul Kahf za'a tsare shi za'a kare shi daga fitinar Masihul Dajjal wanda zai fito a ƙarshen zamani kuma zai yi da'awar Uluhiyya (Allantaka), kuma fitinarsa ita ce mafi girman fitinar da za ta kasance a kan ƙasa tun lokacin da aka halicci (annabi) Adam har zuwa tashin alƙiyama; saboda abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Zai tabbatar masa daga sashin al'amura masu saɓa hankali waɗanda zai fitini wanda ya bi shi, hakan domin cewa farkon Suratul Kahf a cikinta akwai abubuwan mamaki da ayoyi abinda yake yafi girma daga abinda Dujal zai fitini mutane a cikinsa, wanda ya yi tuntuntuni to ba za'a fitina shi da Dujjal ba. A cikin wata riwayar: Ayoyi goma daga ƙarshen surar daga faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Shin waɗanda suka kafirta suna zatan zasu riƙi...}.

Fa'idoji

  • Bayanin falalar Suratul Kahf, kuma cewa (ayoyin) farkonta ko (ayoyin) ƙarshenta suna kiyayewa daga fitinar Dajjal.
  • Labartawa daga al'amarin Dajjal, da bayanin abinda zai tsare shi .
  • Kwaɗaitarwa akan haddace Suratul Kahf cikakkiya, idan ya gajiya to ya haddace ayoyi goman farko da na ƙarshe.
  • AlƘurɗubi ya faɗa a cikin sababin hakan: An ce: Dan abinda ke cikin ƙissar Ashabul Kahf (Ma’abota Kogo) na abubuwan mamaki da ayoyi, wanda ya tsaya a kan su ba zai yi mamakin al'amarin Dajjal ba kuma hakan ba zai shagaltar da shi ba to ba zai fitinu da shi ba, kuma an ce: Saboda faɗinSa ne - Maɗaukakin sarki -: {Domin ya yi gargaɗi da azaba mai tsanani daga gare shi } dan yin riƙo da keɓantar azaba da tsanani daga gare shi , shi ya dace da abinda zai kasance daga Dajjal na da'awar Uluhiyya (allantaka) da rinjayarsa da girman fitinarsa, saboda haka ne tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya girmama al'amarinsa kuma ya gargaɗar daga fitinarsa, sai ma'anar hadisin ta zama: Cewa wanda ya karanta wadannan ayoyin kuma ya yi nazarin ma'anoninsu kuma ya tsaya akaan ma'anoninsu to ya kuɓuta daga gare shi .
Sharhi: العربية

أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن حَفِظ عَشْرَ آيات عن ظَهْرِ قَلْبٍ مِن أول سورة الكهف عُصِم ووُقِي وحُفِظ من فتنةِ المسيح الدجال الذي يَخرج آخر الزمان ويَدَّعي الألوهية، وفتنته أعظم فتنة تكون على الأرض منذ خُلِقَ آدم إلى قيام الساعة؛ لما أمكنه الله عز وجل من بعض الخَوَارِق التي يَفتن بها من تبعه، وذلك لأن أول سورة الكهف فيها من العجائب والآيات ما هو أعظم مما يَفتن الدَّجالُ فيه الناس، فمَن تَدَبَّرَها لم يفتتن بالدجال. وفي رواية: عشر آيات من آخر السورة من قوله تعالى : {أفحسب الذين كفروا أن يتخذوا…}.

  • بيان فضل سورة الكهف، وأن فَوَاتِحَها أو خَوَاتِمَها تَعصم من فتنة الدجال.
  • الإخبار عن أمر الدجال، وبيان ما يعصم منه.
  • الحث على حفظ سورة الكهف كاملةً، فإن عجز فليحفظ العشر الآيات الأولى والأخيرة.
  • قال القرطبي في سَبَبُ ذلك: قيل: لِمَا في قصة أصحاب الكهف من العجائب والآيات، فمَن وَقَفَ عليها لم يَسْتَغرِب أَمْرَ الدجال ولم يَهُلْه ذلك فلم يفتتن به، وقيل: لقوله تعالى: {لينذر بأسًا شديدًا من لدنه} تمسكًا بتخصيص البأس بالشدة واللَّدُنِّيّة، وهو مناسب لما يكون من الدجال من دعوى الإلهية واستيلائه وعظم فتنته، ولذلك عظَّم صلى الله عليه وسلم أمرَه وحَذَّر عنه وتعوذ من فتنته، فيكون معنى الحديث: أن من قرأ هذه الآيات وتدبرها ووقف على معناها حَذِرَه فأمن منه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari