Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، مَا تَرَكْتُ حَاجَّةً وَلَا دَاجَّةً إِلَّا قَدْ أَتَيْتُ، قَالَ: «أَلَيْسَ تَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ؟» ثَلَاثَ مَرَّاتٍ. قَالَ: نَعَمْ، قَالَ: «فَإِنَّ ذَلِكَ يَأْتِي عَلَى ذَلِكَ».
Fassara
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, ban bar wata karamar bukata ko babba ba sai da na zo mata, (na laifi) ya ce: "Shin baka kasance kana shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba kuma cewa Muhammad Manzon Allah ne?" Sau uku. ya ce: Eh, ya ce: "Lallai hakan zai zo akan hakan (wato zai rufe shi )".
Sharhi
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa ni hakika na aikata dukkanin zunubai da sabo, ban bar wani karamin laifi ba ko babba sai da na aikata shi , shin za'a gafarta mini? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Shin baka shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba ?? kuma Muhammad Manzon Allah ne? Ya maimaita masa sau uku. Sai ya amsa masa: Eh ina shaidawa, Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata gare shi - ya ba shi labarin falalar shahada biyu, da kuma kankarewarta ga munanan laifuka, kuma lallai cewa tuba yana kankare abinda ke kafinsa.
Fa'idoji
- Girman (Kalmar) shahada biyu da kuma rinjayarta akan zunubai ga wanda ya fadeta yana mai gaskiya daga zuciyarsa.
- Musulunci yana kankare abinda ke kafinsa.
- Tuba na gaskiya yana shafe abinda ke kafinsa.
- Maimaitawa a cikin ilimantarwa yana daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Falalar (Kalmar) shahada biyu, kuma cewa su sababi ne na tsira daga dawwama a cikin wuta.
Sharhi: العربية
جاء رجلٌ إلى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: يا رسول الله، إني قد فعلت من كل الذنوب والمعاصي، ولم أترك صغيرة ولا كبيرة إلا فعلتها، فهل يُغفَر لي؟ فقال له النبي صلى الله عليه وسلم: ألست تشهد أن لا إله إلا الله وأن محمدًا رسول الله؟ كررها له ثلاث مرات، فأجابه: نعم أشهد، فأخبره النبي صلى الله عليه وسلم بفضل الشهادتين وتكفيرها للسيئات، وأن التوبة تجب ما قبلها.
- عِظم الشَّهادتين ورُجحانها على الذّنوب لمن قالها صادقًا من قلبه.
- الإسلام يجُبُّ ما قبله.
- التّوبة الصّادقة تمحو ما قبلها.
- التّكرار في التّعليم مِن هدي النبي صلى الله عليه وسلم.
- فضل الشهادتين، وأنهما سبب للنجاة من الخلود في النار.