Hadisai

Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ كَذَبَ عَلَيَّ مُتَعَمِّدًا فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya yi masa karya da gangan ta hanyar danganta masa magana ko aiki, to lallai cewa shi yana da mazauni a wuta; sakamako ne gare shi akan karyar da ya yi masa.

Fa'idoji

  • Karya ga - Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da nufi da ganganci sababi ne na shiga wuta.
  • Karya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba kamar karya ce ga sauran mutane ba, saboda abinda ke tattare da hakan na barnace-barnace masu girma a Addini da duniya.
  • Tsoratarwa akan yada hadisai kafin tabbatar da ingancin dangantasu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن كَذَبَ عليه مُتعمدًا بنِسبةِ قولٍ أو فعلٍ له كَذبًا، فإنّ له في الآخرة مَجلسًا في النار؛ جزاء له على كذبه عليه.

  • الكَذب على النبيِّ صلى الله عليه وسلم بالقصد والعَمْد سببٌ لدخول النار.
  • الكذب على النبي عليه الصلاة والسلام ليس كالكذب على سائر الناس، لِمَا يَترتَّب على ذلك من مفاسد عظيمة في الدين والدنيا.
  • التحذير من نشر الأحاديث قبل التثبُّت والتأكد من صحة نسبتها إلى النبي صلى الله عليه وسلم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari