Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ: «سَيَكُونُ فِي آخِرِ أُمَّتِي أُنَاسٌ يُحَدِّثُونَكُمْ مَا لَمْ تَسْمَعُوا أَنْتُمْ وَلَا آبَاؤُكُمْ، فَإِيَّاكُمْ وَإِيَّاهُمْ».
Fassara
Daga Abu Huraira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - lallai ya ce: "Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su"
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wasu mutane a ƙarshen al'ummata za su bayyana suna ƙirƙirar ƙarya, kuma suna faɗin abin da wani kafinsu bai faɗa ba, suna ba da labarai da hadisan ƙarya abubuwan ƙirƙira, sai (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya umarcemu mu nisancesu kada mu zauna da su, kuma kada mu ji hadisansu; don kada ƙirƙirarran hadisin ya tabbata a cikin zukata, sai mu kasa kuɓuta daga su.
Fa'idoji
- A cikinsa akwai alama daga alamonin Annabta, yayin da Annabi - tsira da aminin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labain abin da zai afku a cikin al'ummarsa, sai ya afku kamar yadda ya ba da labari.
- Nisantar wanda zai yi ƙarya ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - haka kuma [da yin ta] ga Addinin Musulunci, da [buƙatar] kada a saurari ƙaryarsu.
- Gargaɗi game da karɓar Hadisai ko yaɗa su sai bayan tabbatarwa game da ingancinsu da tabbatarsu.
Sharhi: العربية
أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم بأنه سيَظهر أُناسٌ في آخِر أُمتِه يَفْتَرون الكذب، ويقولون ما لم يقلْه أحدٌ من قبلهم، فيُخبِرون بالأحاديث المكذوبة والمُخْتَلَقة، فأمَرَنا عليه الصلاة والسلام أنْ نَبْتَعِدَ عنهم ولا نجالسهم، ولا نسمع أحاديثهم؛ لئلا يتقرر ذلك الحديث المختلق في النفوس، فنعجز عن التخلُّص منه.
- فيه عَلَم من أعلام النبوة، حيث إن النبي صلى الله عليه وسلم أخبر بما سيقع في أمته، فكان كما أخبر.
- الابتعاد عمّن يَكْذِبُ على رسول الله صلى الله عليه وسلم وعلى دين الإسلام، وعدم الاستماع لكذبهم.
- التحذير من قبولِ الأحاديث أو نشرِها إلا بعد التأكُّد من صحتِها وثبوتِها.