Hadisai

Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبي هريرة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «حَقٌّ عَلَى كُلِّ مُسْلِمٍ أَنْ يَغْتَسِلَ فِي كُلِّ سَبْعَةِ أَيَّامٍ يَوْمًا، يَغْسِلُ فِيهِ رَأْسَهُ وَجَسَدَهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa".

Sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wajibi ne mai ƙarfi a kan kowanne musulmi baligi mai hankali ya yi wanka a kowanne kwana bakwai daga sati rana ɗaya, sai ya wanke kansa da jikinsa a wannan ranar; don neman tsarki da tsafta, mafi cancantar waɗannan kwanukan (ita ce) ranar Juma'a, kamar yadda aka fahimta daga sashin riwayoyi, wanka ranar Juma'a kafin sallah mustahabbi ne mai ƙarfi, ko da ya yi wanka ranar Alhamis misali, abinda ya cire shi daga wajabcin (shi ne) faɗin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -: "Mutane sun kasance suna wa kawunansu hidima, sun kasance idan sun tafi zuwa Juma'a sai su tafi a yanayinsu: sai aka ce da su: Ina ma dai kun yi wanka". Bukhari ne ya ruwaito shi, a cikin wata riwayar ta shi: "A tare da su akwai wari" wato warin gumi da makamanncin hakan, a tare da hakan aka ce da su: Ina ma dai kun yi wanka

Fa'idoji

  • Damuwa da kulawar musulunci game da tsafta da kuma tsarki.
  • Wankan Juma'a mustahabbi ne mai ƙarfi don yin sallah.
  • Ambaton kai ko da ambaton jiki ya tattaroshi; don ba shi muhimmanci ne.
  • Wanka yana wajaba a kan duk wanda aka samu a tare da shi akwai wari abin ƙi wanda mutane suke cutuwa da shi.
  • Mafi ƙarfin yini don yin wanka (shi ne) ranar Juma'a don falalarta
Sharhi: العربية

أَخْبَرَ رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: أنه حقٌّ متأكد على كل مسلم بالغ عاقل أنْ يغتسلَ في كل سبعة أيام من الأسبوع يومًا، فيغسل في هذا اليوم رأسَه وجسدَه، طلبًا للطهارة والنظافة، وأَولى هذه الأيام يومُ الجمعة، كما يُفهم من بعض الروايات، والاغتسال يوم الجمعة قبل الصلاة مستحب استحبابًا مؤكدًا، ولو كان اغتسل يوم الخميس مثلًا، والصارف عن الوجوب قول عائشة رضي الله عنها: "كان الناسُ مَهَنَةَ أنفسهم، وكانوا إذا راحوا إلى الجمعة راحوا في هيئتهم: فقيل لهم: لو اغتسلتم"، رواه البخاري، وفي رواية له: "لهم أرواح" أي رائحة العَرَقِ ونحوِه، ومع ذلك قيل لهم "لو اغتسلتم"، فغيرُهم من باب أولى.

  • اهتمام وعناية الإسلام بالنظافة والطهارة.
  • غسل الجمعة مستحب استحبابًا مُؤكدًا للصلاة.
  • ذِكْر الرَّأس وإن كان ذِكْر الجسد يشمله؛ للاهتمام به.
  • ﻳﺠﺐ ﺍﻟﻐﺴﻞ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﻦ ﻭُﺟِﺪﺕْ ﺑﻪ ﺭﺍﺋﺤﺔٌ ﻛﺮﻳﻬﺔٌ ﻳﺘﺄﺫﻯ ﺑﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎس.
  • آكَدُ يومٍ للاغتسال يوم الجمعة؛ لفضله.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari