Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ: أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «صَلَاةٌ فِي مَسْجِدِي هَذَا خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ صَلَاةٍ فِيمَا سِوَاهُ إِلَّا الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ».
Fassara
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar sallah a masallacinsa, kuma cewa shi yafi yawan lada daga sallah dubu a cikin waninsa daga masallatan duniya, sai dai Masallaci mai alfarma a Makka, shi ne mafifici daga sallah a cikin masallacinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Fa'idoji
- Ruɓanya ladan sallah a cikin Masallaci mai alfarma, da masallacin Annabi.
- Sallah a Masallaci mai alfarma ita ce mafi alheri daga sallah dubu a wasu masallatan da ba su ba.
Sharhi: العربية
بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم فضْلَ الصلاةِ في مسجده، وأنه أفضل ثوابًا من ألف صلاة فيما سواه من مساجد الأرض، إلا المسجد الحرام بمكة، فهي أفضل من الصلاة في مسجده صلى الله عليه وسلم.
- مُضاعَفة أجر الصلاة في المسجد الحرام، والمسجد النبوي.
- الصلاةَ في المسجد الحرام خيرٌ مِن مائة ألفِ صلاةٍ في غيره مِن المساجد.