Hadisai

Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رَضيَ اللهُ عنهُ: أَنَّ رَجُلًا سَمِعَ رَجُلًا يَقْرَأُ: {قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ} يُرَدِّدُهَا، فَلَمَّا أَصْبَحَ جَاءَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَذَكَرَ ذَلِكَ لَهُ، وَكَأَنَّ الرَّجُلَ يَتَقَالُّهَا، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ إِنَّهَا لَتَعْدِلُ ثُلُثَ القُرْآنِ».

Fassara

Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya ji wani mutum yana karanta: {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai}, yana maimaita ta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya fada masa hakan, kai ka ce mutumin yana ganin ƙanƙantarta, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda raina yake hannunSa, lallai cewa ita ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani".

Sharhi

Abu Sa'id al-Khudr - Allah Ya yarda da shi - ya fadi cewa wani mutum ya ji wani mutumin daban yana karanta Suratu (Ikhlas): {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai} yana maimaitata a kowanne dare ba ya ƙari akanta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo gurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ambata masa haka, kamar shi mai maganar yana ganin cewa ta yi kaɗan, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan ma'anar ƙarfafawa: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai cewa ita (Surar) ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.

Fa'idoji

  • Falalar Suratul Ikhlas, kuma ita tana daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.
  • Halaccin karatu a sallar tsayuwar dare koda da ayoyi kaɗan ne da kuma maimaita su, da rashin ƙaranta hakan.
  • AlMaziri ya ce: An ce: Ma'anarsa: Cewa Alƙur'ani yana da ɓangarori uku; Kissoshi da hukunce-hukunce da kuma siffofin Allah - Maɗaukakin sarki -, {Ka ce Shi ne Allah Makaɗaici} mai tacewa ce - yana nufin ga siffofin Allah -, dan haka ita ce ɗaya bisa uku, kuma wani yanki daga cikin yankuna uku. Kum an ce: Ma'narsa: Cewa ladan karantata ana ninka shi da gwargwadan ladan karatun ɗaya bisa uku na Alƙur'ani ba tare da ninkawa ba.
Sharhi: العربية

ذكر أبو سعيد الخدري رضي الله عنه أن رجلًا سمع آخر يقرأ سورة: {قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ} يرددها كل الليل لا يزيد عليها، فلما أصبح جاء إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فذكر ذلك له، وكأن السائل يرى أنها قليلة، فقال صلى الله عليه وسلم يمينًا على معنى التأكيد: والذي نفسي بيده إنها تساوي ثلث القرآن.

  • فضل سورة الإخلاص، وأنها تعدِل ثلث القرآن.
  • جواز القراءة في قيام الليل ولو بيسير الآيات وترديدها، وعدم تقليل ذلك.
  • قال المازري: قيل: معناه: أن القرآن على ثلاثة أنحاء؛ قصص وأحكام وصفات لله تعالى، و{قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ} متمحضة -يعني لصفات الله-، فهي ثلث، وجزء من ثلاثة أجزاء، وقيل: معناه: أن ثواب قراءتها يضاعف بقدر ثواب قراءة ثلث القرآن بغير تضعيف.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari