Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَجُلًا مِنَ اليَهُودِ قَالَ لَهُ: يَا أَمِيرَ المُؤْمِنِينَ، آيَةٌ فِي كِتَابِكُمْ تَقْرَؤُونَهَا، لَوْ عَلَيْنَا مَعْشَرَ اليَهُودِ نَزَلَتْ لاَتَّخَذْنَا ذَلِكَ اليَوْمَ عِيدًا، قَالَ: أَيُّ آيَةٍ؟ قَالَ: {اليَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإِسْلاَمَ دِينًا} [المائدة: 3] قَالَ عُمَرُ: قَدْ عَرَفْنَا ذَلِكَ اليَوْمَ، وَالمَكَانَ الَّذِي نَزَلَتْ فِيهِ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَهُوَ قَائِمٌ بِعَرَفَةَ يَوْمَ جُمُعَةٍ.
Fassara
Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum daga cikin Yahudawa ya ce masa: Yakai sarkin muminai, Wata aya a cikin littafinku kuna karantata, da a ce agurinmu mu Yahudawa ta sauka da mun riƙi ranar idi, ya ce: Wacce aya ce? ya ce: {A yau ne na cika muku Addininku kuma na cika muku ni'imata kuma na yardar muku da Musulunci a matsayin Addini} [al-Ma'ida: 3] Umar ya ce: Haƙiƙa mun san wannan ranar, da gurin da ta sauka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa alhali shi yana tsaye a Arfa a ranar Juma'a.
Sharhi
Wani mutum daga cikin Yahudawa ya zo gurin sarkin muminai Umar - Allah Ya yarda da shi - kuma ya ce masa: Wata aya ce da kuke karantata a cikin littafinku Alƙur'ani, da ace mu jama'ar Yahudawa ne ta sauka a garemu a cikin littafinmu Attaura da mun maida wannar ranar idin da zamu dinga taruwa da shi; dan godiya ga ni'imar saukar wannan ayar mai girma, sai Umar - Allah Ya yardada shi - yace masa: Wace aya ce? Ya ce: {Kuma yaune Na cika muku Addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin Addini} Sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Haƙiƙa mun san wannan ranar, da gurin da ayar mai girma ta sauka a cikinsa, haƙiƙa ta saukane ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -a ranar idi, ita ce ranar Juma'a alhali shi yana tsaye a Arfa, kuma su ranaku biyu ne masu girma a wurin musulmai.
Fa'idoji
- Bayanin abin da Umar - Allah Ya yarda da shi - yake a kansa na kulawa da wurin da ayar ta sauka da kuma lokacinta.
- Wannan ayar a cikinta akwai bayanin abin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi baiwa da shi ga wannan al'ummar, inda Ya cika mata Addininta, kuma Ya cika mata ni'imominSa, yadda bata buƙatar wani ƙari a cikin al'amarin Addini, duk abin da ya faru bayan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya cika shi, in da ba shi da wani dalili daga gare shi da ake la'akari da shi (a matsayin) bidi'a ɓatacciya, kamar yadda hakan ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya farar (da wani abu) a cikin al'amarinmu wannan abin da ba ya daga cikinsa, to shi abin juyarwa ne".
- Wannan hadisin za'a iya fahima daga gare shi cewa bukukuwan Idi basa kasancewa da ra'ayi da kuma ƙirƙira kamar yadda wasu daga cikin mazowa Littafi (Yahudawa da Nasara) daga gabaninmu suke aikata shi; kawai yana kasancewa ne da shari'a da kuma bi, to wannan ayar yayin da ta ƙunshi cika Addini da cika ni'imar da Allah Ya saukar da ita a cikin ranar da ya shara'antata idi ga wannan al'ummar ta fuska biyu: Na farkonsu: Cewa ita ce ranar idin mako ita ce ranar Juma'a. Na biyu: Ita ce ranar idin babbaban taro , ita ce lokacin taruwarsu mafi girma kuma wurin tsayuwarsu mafi girma (wato Arafat, ga Musulmai).
- Sa'adi ya faɗa a cikin tafsirin wannan ayar: {A yau ne Na cika muku Addininku} ta hanyar cikar nasara, da cika shari'u na zahiri da baɗini, tushe da kuma rassa, saboda haka ne Alkur’ani da Hadisi suka kasance sun isa dukkanin isa a cikin hukunce-hukuncen Addini, tushensa da kuma rassansa, duk mai ɗorawa kansa aiki wanda yake riya cewa babu makawa ga mutane a cikin sanin aƙidunsu da kuma hukunce-hukuncensu zuwa wasu ilimai waɗanda ba ilimin Littafi da sunnah ba, na ilmul kalam da waninsa, to shi jahili ne, mai ɓarna a cikin da'awarsa, ya riya cewa Addini ba ya cika sai da abin da ya faɗe shi kuma ya yi kira zuwa gare shi, wannan yana daga cikin mafi girman zalinci da dangantawa Allah da ManzonSa jahilci, {Kuma Na cika muku ni'imata} ta zahiri da baɗini {Kuma na yardar muku da Musulunci a matsayin Addini} wato: Na zaɓar muku shi a matsayin Addini, kamar yadda na yardar muku da shi, sai ku tsaya a kansa dan godiya ga Ubangijinku, ku gode maSa abin da Ya yi muku baiwa da mafificin Addinai kuma mafi ɗaukakarsu kuma mafi cikarsu.
Sharhi: العربية
جاء رجل من اليهود إلى أمير المؤمنين عمر رضي الله عنه وقال له: آية في كتابكم القرآن تقرؤونها، لو نزلت علينا -معشر اليهود- في كتابنا التوراة لجعلنا ذلك اليوم عيدًا نحتفل به؛ شكرًا لنعمة نزول هذه الآية العظيمة، فقال له عمر رضي الله عنه: أي آية؟ قال: {اليَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإِسْلاَمَ دِينًا}. فقال عمر رضي الله عنه: قد عرفنا ذلك اليوم، والمكان الذي نزلت فيه هذه الآية الكريمة، فهي قد نزلت يوم عيد، وهو يوم الجمعة على النبي صلى الله عليه وسلم وهو قائم بعرفة، وهما يومان عظيمان عند المسلمين.
- بيان ما كان عليه عمر رضي الله عنه من العناية بمكان نزول الآية وزمانها.
- هذه الآية فيها بيان ما مَنَّ الله تعالى به على هذه الأمة حيث أكمل دينها، وأتمَّ نِعمَه عليها، بحيث لا تحتاج إلى زيادة في أمر الدين، فكل ما حدث بعد أن أكمله الله تعالى، مما لا دليل له منه يعتبر بدعة ضلالة، كما ثبت ذلك عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: "من أحدث في أمرنا هذا ما ليس منه، فهو رد".
- هذا الحديث قد يؤخذ منه أن الأعياد لا تكون بالرأي والاختراع كما يفعله أهل الكتابين من قبلنا؛ إنما تكون بالشرع والاتباع، فهذه الآية لما تضمنت إكمال الدين وإتمام النعمة أنزلها الله في يوم شرعه عيدًا لهذه الأمة من وجهين: أحدهما: أنه يوم عيد الأسبوع وهو يوم الجمعة. والثاني: أنه يوم عيد أهل الموسم، وهو يوم مجمعهم الأكبر وموقفهم الأعظم.
- قال السعدي في تفسير هذه الآية: {اليَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ} بتمام النصر، وتكميل الشرائع الظاهرة والباطنة، الأصول والفروع، ولهذا كان الكتاب والسنة كافيين كل الكفاية، في أحكام الدين أصوله وفروعه، فكل متكلّف يزعم أنه لا بد للناس في معرفة عقائدهم وأحكامهم إلى علوم غير علم الكتاب والسنة، من علم الكلام وغيره، فهو جاهل، مبطل في دعواه، قد زعم أن الدين لا يكمل إلا بما قاله ودعا إليه، وهذا من أعظم الظلم والتجهيل لله ولرسوله، {وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي} الظاهرة والباطنة {وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ دِينًا} أي: اخترته واصطفيته لكم دينًا، كما ارتضيتكم له، فقوموا به شكرًا لربكم، واحمدوا الذي مَنَّ عليكم بأفضل الأديان وأشرفها وأكملها.