Hadisai

Idan ɗayanku ya shiga masallaci to ya yi wa Annabi salati kuma ya ce: Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Hasan neIbnu Majah da Hakim ne suka Rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمْ المَسْجِدَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ، وَإِذَا خَرَجَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ اعْصِمْنِي مِنْ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ»، وَلِلْحَاكِمِ: «وَإِذَا خَرَجَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ أَجِرْنِي مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ».

Fassara

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Idan ɗayanku ya shiga masallaci to ya yi wa Annabi salati kuma ya ce: Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa, idan kuma zai fita to ya yi wa Annabi sallama sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa». (Riwayar) Hakim: «Idan zai fita to ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da musulmi cewa idan ya yi nufin shiga masallaci ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - salati da faɗinsa: Ya Allah Ka yi tsira Ka yi aminci ga (Annabi) Muhammad, sannan ya ce: (Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa). Idan zai fita to ya yi wa Annabi salati sai ya ce: (Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa). A cikin riwayar Hakim: Sai ya ce: (Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa).

Fa'idoji

  • An so wannan adddu'ar a yayin shiga masallaci da fita daga cikinsa.
  • Gamamman Zikirin ne a kowanne masallaci har Masallaci mai alfarma.
  • Keɓance ambatan rahama da shiga, da kuma tsari daga Shaiɗan a fita: Cewa mai shiga zai shagaltu da abin da zai kusanto da shi zuwa ga Allah da kuma aljannarSa sai ya dace da ya ambaci rahama, idan zai fita to shi zai shiga duniya da abin da ke cikinta na abubuwan shagaltarwa, sai ya dace da ya nemi kariya da kiyayewar Allah daga Shaiɗan.
Sharhi: العربية

أرشد النبي صلى الله عليه وسلم المسلم إذا أراد الدخول إلى المسجد أن يسلم على النبي صلى الله عليه وسلم بقوله: اللهم صل وسلم على محمد، ثم ليقل: (اللهم افتح لي أبواب رحمتك). وإذا خرج فليسلم على النبي وليقل: (اللهم اعصمني من الشيطان الرجيم)، وفي رواية للحاكم: وليقل: (اللهم أجرني من الشيطان الرجيم).

  • استحباب هذا الدعاء عند دخول المسجد والخروج منه.
  • الذكر عام في كل المساجد، حتى المسجد الحرام.
  • تخصيص ذكر الرَّحمة بالدُّخول، والعصمة من الشيطان بالخروج: أنّ الدَّاخل اشتغل بما يقرِّبه إلى الله وإلى جنته فناسَب أن يذكُر الرَّحمة، فإذا خرج فإنه ينطلق في الدنيا بما فيها من ملهيات ومشغلات، فناسب أن يطلب من الله الحماية والحفظ من الشيطان.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari