Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «البَسُوا مِنْ ثِيَابِكُمُ البَيَاضَ، فَإِنَّهَا مِنْ خَيْرِ ثِيَابِكُمْ، وَكَفِّنُوا فِيهَا مَوْتَاكُمْ».
Fassara
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku sanya farare daga tufafinku, domin cewa sune mafi alherin tufafinku, kuma ku yi wa mamatanku likkafani a cikinsu".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana shiryar da maza cewa su sa tafafi masu farin launi da kuma yi wa mamata likkafani a cikinsu; domin cewa sune mafi alherin tufafi.
Fa'idoji
- An so sanya farin tufafi, kuma waninsa na wata kalar ma yana halatta.
- An so yi wa mamata likkafani da fararen (tufafi).
- Shaukani ya ce: Hadisin yana nuni akan halaccin sanya fari da yi wa mamata likkafani da shi; kasancewarsa ya fi waninsa tsarkaka, amma kasancewarsa ya fi tsarki to wannan zahiri ne, amma kasancewarsa ya fi tsafta domin cewa mafi ƙanƙatar abu idan ya faɗa kansa zai bayyana sai ya fifita.
Sharhi: العربية
يرشد النبي صلى الله عليه وسلم الرجال بلبس الثياب ذات اللون الأبيض وتكفين الموتى فيها؛ فإنها من خير الثياب.
- استحباب لبس الثوب الأبيض، ويجوز غيره من الألوان.
- استحباب تكفين الموتى بالبياض.
- قال الشوكاني: والحديث يدل على مشروعية لبس البياض وتكفين الموتى به؛ كونه أطهر من غيره وأطيب، أما كونه أطيب فظاهر، وأما كونه أطهر فلأن أدنى شيء يقع عليه يظهر فيفضل.