Hadisai

Ku bibiyi tsakanin Hajji da Umarah, domin cewa su suna kore talauci da kuma zunubai kamar yadda zugazagi yake kore dattin ƙarfe, da zinariya, da azirfa, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neTirmizi da Nasa'i da Ahmad ne Suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «تَابِعُوا بَيْنَ الحَجِّ وَالعُمْرَةِ، فَإِنَّهُمَا يَنْفِيَانِ الفَقْرَ وَالذُّنُوبَ كَمَا يَنْفِي الكِيرُ خَبَثَ الحَدِيدِ، وَالذَّهَبِ، وَالفِضَّةِ، وَلَيْسَ لِلْحَجَّةِ الْمَبْرُورَةِ ثَوَابٌ إِلاَّ الجَنَّةُ».

Fassara

An karbo daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku bibiyi tsakanin Hajji da Umarah, domin cewa su suna kore talauci da kuma zunubai kamar yadda zugazagi yake kore dattin ƙarfe, da zinariya, da azirfa, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan kusantowa tsakanin yin ibadun Hajji da kuma yin Umarah da rashin yankewa daga yinsu tare da iko, domin cewa yin su yana zama sababi na kawar da talauci da zunubai da kuma tasirinsu a cikin zuciya, kamar yadda zugazugi na wuta yana zamowa sababi a cikin kawar da dattin ƙarfe da abinda yake cakuɗuwa da shi na ma'adanan da su ba daga gare shi suke ba.

Fa'idoji

  • Falalar bibiya tsakaknin Hajji da Umarah da kuma kwaɗaitarwa akan hakan.
  • Bibiyar Hajji da Umarah yana daga sabubban wadata da kuma gafarta zunubai.
  • Al-Mubarakfuri ya ce: (Suna kore talauci) wato Suna gusar da shi, hakan yana ɗaukar talauci na zahiri ta hanyar samun wadatar hannu, da kuma talauci na baɗini ta hanyar samun wadatar zuci.
Sharhi: العربية

حث النبي صلى الله عليه وسلم على المقاربة بين أداء نسك الحج ونسك العمرة وعدم الانقطاع عن أدائهما مع الاستطاعة، لأن أداءهما يكون سببًا في إزالة الفقر والذنوب وأثرها في القلب، كما أن نفخ النار يكون سببًا في إزالة وسَخ الحديد وما يخالطه من معادن ليست منه.

  • فضل المتابعة بين الحج والعمرة والحث على ذلك.
  • متابعة الحج والعمرة من أسباب الغنى ومغفرة الذنوب.
  • قال المباركفوري: (ينفيان الفقر) أي يزيلانه، وهو يحتمل الفقر الظاهر بحصول غنى اليد، والفقر الباطن بحصول غنى القلب.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari