Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أَتِمُّوا الصَّفَّ المُقَدَّمَ، ثُمَّ الَّذِي يَلِيهِ، فَمَا كَانَ مِنْ نَقْصٍ فَلْيَكُنْ فِي الصَّفِّ المُؤَخَّرِ».
Fassara
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku cika sawun gaba, sannan wanda ke biye da shi, abin da aka samu tawaya daga gare shi to ya zama a cikin sawun ƙarshe ne».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci mazaje masu yin sallah a jam'i da cika sawun farko, sannan da cika sawun da ke biye da shi, idan za’a samu wata tawaya a cikin wani sawu to wannan tawayar ta zama a sawun ƙarshe ne.
Fa'idoji
- Bayanin sunna a kan daidaita sawu.
- Ya wajaba akan masallata kada su bar tawaya a cikin sawun gaba, kai tawaya ta zama a cikin sawun ƙarshe ne.
Sharhi: العربية
أَمَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم الرجال المصلين جماعة بإكمال الصف الأول، ثم بتكميل الصف الذي يليه، وهكذا، فإذا وجد نقص في صف فليكن هذا النقص في الصف الأخير.
- بيان السنة في تسوية الصفوف.
- على المصلين ألا يتركوا النقص في الصفوف المقدمة، بل يكون النقص في الصف الأخير.