Hadisai

Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙaryarsu kuma ya taimakesu akan zalincinsu to ba ya ta tare da ni, nima bana tare da shi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAhmad ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ حُذَيْفَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّهَا سَتَكُونُ أُمَرَاءُ يَكْذِبُونَ وَيَظْلِمُونَ، فَمَنْ صَدَّقَهُمْ بِكَذِبِهِمْ وَأَعَانَهُمْ عَلَى ظُلْمِهِمْ فَلَيْسَ مِنَّي، وَلَسْتُ مِنْهُ، وَلَا يَرِدُ عَلَيَّ الْحَوْضَ، وَمَنْ لَمْ يُصَدِّقْهُمْ بِكَذِبِهِمْ وَلَمْ يُعِنْهُمْ عَلَى ظُلْمِهِمْ فَهُوَ مِنِّي، وَأَنَا مِنْهُ، وَسَيَرِدُ عَلَيَّ الْحَوْضَ».

Fassara

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙaryarsu kuma ya taimakesu akan zalincinsu to ba ya ta tare da ni, nima bana tare da shi, kuma ba zai gangarowa Alkausara ba, wanda bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to shi yana tare da ni, nima ina tare da shi, kuma zai zo Alkausara".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu shagabanni da zasu shugabanci mutane bayan rasuwarsa zasu dinga ƙarya a magana sai su dinga faɗin abinda ba sa aikatawa, kuma suna zalinci a cikin hukunci, wanda ya shiga gurinsu ya gasgata su akan ƙaryarsu, kuma ya taimakesu da aikata zalinci ko faɗarsa, kamar ba su fatawa dan neman kusancinsu da kwaɗayin abinda ke hannunsu; to ni babu ruwana da shi, ba shi ba ni, ba ni ba shi, kuma ba zai zo Alkausara ba ranar alƙiyama. Wanda bai shige su ba , kuma bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to yana tare da ni, kuma zai zo Alkausara ranar alƙiyama ba.

Fa'idoji

  • Shugabanni idan an shiga gurinsu dan fadakarwa da shiryarwa da sauƙaƙa sharri; wannan shi ne abin nema, amma idan ya shiga gurinsu dan ya taimakesu akan zalinci kuma ya gasgatasu da ƙarya to wannan shi ne abin zargi.
  • Bayanin narko na azaba ga wanda ya taimaki wani shugaba akan zalincinsa.
  • Wannan narkon a cikin Hadisin yana nuni akan haramcin wannan aikin, kuma hakan yana daga cikin manyan zunubai.
  • Kwaɗaitarwa a kan taimakekeniya akan aikin alheri da kuma tsoron Allah, da rashin taimakekeniya a kan zunubi da shisshigi.
  • Tabbatar da tafkin Alkausara ga Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma lallai cewa al'ummarsa zasu gangaro zuwa gare shi.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أنه سيتولى على الناس بعد موته أمراء يَكذبون في الكلام فيقولون ما لا يفعلون، ويظلمون في الحكم، فمن دخل عليهم وصدّقهم بكذبهم، أو أعانهم بفعل الظلم أو قوله كالإفتاء لهم تقرُّبًا لهم ورجاء ما عندهم؛ فأنا بريء منه وليس مني، ولست منه، ولا يأتي عليّ حوض الكوثر يوم القيامة، ومن لم يدخل عليهم ويصدقهم بكذبهم ويعنهم على ظلمهم فهو مني، وأنا منه، وسيرد علي الحوض يوم القيامة.

  • السلاطين إذا دُخِلَ عليهم بالتوجيه والإرشاد وتخفيف الشر؛ هذا هو المطلوب، أما إذا دخل عليهم ليعينهم على الظلم ويصدقهم بالكذب فهذا هو المذموم.
  • بيان الوعيد لمن أعان أميرًا على ظلمه.
  • هذا الوعيد في الحديث يدل على تحريم هذا الفعل، وأنه من كبائر الذنوب.
  • الحث على التعاون على البر والتقوى، وعدم التعاون على الإثم والعدوان.
  • إثبات الحوض لنبينا محمد صلى الله عليه وسلم، وأن أمته تَرِدُ عليه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari