Hadisai

Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي شُرَيْحٍ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «وَاللَّهِ لاَ يُؤْمِنُ، وَاللَّهِ لاَ يُؤْمِنُ، وَاللَّهِ لاَ يُؤْمِنُ»، قِيلَ: وَمَنْ يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ قَالَ: «الَّذِي لاَ يَأْمَنُ جَارُهُ بَوَايِقَهُ».

Fassara

Daga Abu Shuraih - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba mumini ba ne», aka ce: Waye ya Manzon Allah? ya ce: «Wanda maƙocinsa ba ya aminta daga sharrinsa».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa kuma ya ƙarfafi rantsuwarsa sau uku, sai ya ce: Wallahi ba mumini ba ne, wallahi ba muminin ba ne, wallahi ba mumini ba ne, sai sahabbai suka tambaye shi : Waye wanda ba mumini ba ya Manzon Allah? ya ce: Wanda maƙocinsa yake jin tsoron yaudararsa da zalincinsa da kuma sharrinsa.

Fa'idoji

  • Kore imani ga wanda maƙocinsa ba ya aminta daga zalincinsa da sharrinsa yana nuni akan cewa shi yana daga manyan zunubai, kuma cewa mai aikata shi mai tauyayyen imani ne.
  • Kwaɗaitarwa mai ƙarfi akan kyautatawa maƙoci da barin cutar da shi da magana ne ko da aiki.
Sharhi: العربية

أقسمَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم وأكّد قسمه ثلاث مرات، فقال: والله لا يؤمن، والله لا يؤمن، والله لا يؤمن، فسأله الصحابة: ومن الذي لا يؤمن يا رسول الله؟ قال: الذي يخاف جاره من غدره وظلمه وشره.

  • نفي الإيمان عمن لا يأمن جاره من ظلمه وشره يدل على أنه من الكبائر، وعلى أن فاعله ناقص الإيمان.
  • الحض الأكيد على الإحسان إلى الجار وترك أذاه بالقول أو الفعل.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari