Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ: «لَا يَمْنَعَنَّ رَجُلًا مِنْكُمْ مَخَافَةُ النَّاسِ أَنْ يَتَكَلَّمَ بِالْحَقِّ إِذَا رَآهُ أَوْ عَلِمَهُ».
Fassara
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa».
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa huɗuba, daga cikin abinda ya yi musu wasicci da shi cewa kada tsoro da kwarjinin mutane da kuma ƙarfinsu ya hana musulmi faɗin gaskiya ko umarni da ita idan ya ganta ko ya santa.
Fa'idoji
- Kwaɗaitarwa akan bayyanar da gaskiya da kuma rashin ɓoyeta dan jin tsoron mutane.
- Faɗin gaskiya ba ya nufin rashin lazimtar ladabi ta hanyar faɗinta da kuma hikima da kyakkyawan wa'azi a cikinta.
- Wajabcin inkarin munkari, da kuma gabatar da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - akan mas'lahohin mutane waɗanda sukaci karo da ita.
Sharhi: العربية
خَطَبَ النبي صلى الله عليه وسلم في أصحابه ومما أوصى به أن لا يمنع المسلم مخافة ومهابة الناس وشوكتهم أن يترك قول الحق أو الأمر به إذا رآه أو علمه.
- الحث على إظهار الحق وعدم كتمه خوفًا من الناس.
- قول الحق لا يعني عدم الالتزام بالأدب في طريقة قوله والحكمة والموعظة الحسنة فيه.
- وجوب إنكار المنكر، وتقديم حق الله تعالى على مصالح الناس المعارضة له.