Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أبي سَلَمَةَ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ أَنَّ جَابِرَ بْنَ عَبْدِ اللَّهِ الأَنْصَارِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: وَهُوَ يُحَدِّثُ عَنْ فَتْرَةِ الوَحْيِ، فَقَالَ فِي حَدِيثِهِ: «بَيْنَا أَنَا أَمْشِي إِذْ سَمِعْتُ صَوْتًا مِنَ السَّمَاءِ، فَرَفَعْتُ بَصَرِي، فَإِذَا المَلَكُ الَّذِي جَاءَنِي بِحِرَاءٍ جَالِسٌ عَلَى كُرْسِيٍّ بَيْنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ، فَرُعِبْتُ مِنْهُ، فَرَجَعْتُ فَقُلْتُ: زَمِّلُونِي، فَأَنْزَلَ اللَّهُ تَعَالَى: {يَا أَيُّهَا المُدَّثِّرُ1 قُمْ فَأَنْذِرْ} [المدثر: 2] إِلَى قَوْلِهِ {وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْ} [المدثر: 5]. فَحَمِيَ الوَحْيُ وَتَتَابَعَ».
Fassara
Daga Abu Salama Ibnu Abdurrahman cewa Jabir Ibnu Abdullahi al-Ansari - Allah Ya yarda da su - ya ce: Alhali shi yana bada labari game da lokacin wahayi, a cikin zancensa sai ya ce: "Wata rana ina tafiya sai na ji wata ƙara daga sama, sai na ɗaga ido na, sai ga mala'ikan da ya zo mini a (kogon) Hira a zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, ai na ji tsoronsa, sai na dawo sai na ce: Ki lulluɓeni, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da {Ya kai mai lulluɓa1 Ka tashi ka yi gargaɗi}[alMuddasir: 2] zuwa faɗinSa: {Ka ƙauracewa gumaka} [al-Muddassir: 5]. Sai wahayi ya tsananta kuma ya bibiyi juna.
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari alhali shi yana bada labari game da tsayawar wahayi da kuma dakatar da saukarsa a farkon manzancinsa: Wata rana ina tafiya a lungun Makka sai na ji wata ƙara daga sama sai na ɗaga idona, sai ga mala'ikan da ya zo mini a kogon Hira yana zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, sai na tsorata na razana daga gare shi, sai na dawowa iyalina sai na ce: Ku lulluɓeni da tufafi. Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da: {Ya kai mai lulluɓa} mai lulluɓa da tufansa, {Ka ta shi} da kira {Ka yi gargaɗi} ka gargaɗar da wanda bai yi imani da saƙonka ba. {Ubangijinka} Ubangijinka abin bauta {Ka girmama} ka gode maSa ka girmamaShi. {Tufafinka} tufafinka {Ka tsarkake} ka tsamosu daga najasa, {Gumaka} da bautar gumaka da mutun mutumi {To ka ƙaurace} ka bari, sai wahayi ya yi ƙarfi bayan haka ya yi yawa.
Fa'idoji
- Yankewar wahayi ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bayan saukar faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -: {Ka yi karatu}.
- Halaccin mutum ya bada labarin abin da ya faru gare shi na jarawaba bayan gushewar jarabawar, dan godiya ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Farkon abin da ya sauka shine faɗinSa: {Yakai mai lulluɓa} bayan saukar: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta}.
- Falalar Allah - tsarki ya tabbatara maSa Ya ɗaukaka - ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - inda ya zuba wahayinSa ba tare da yankewa ba har sai da yabar duniya.
- Wajabcin tsayuwa da kira zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da yi wa waɗanda suka bijire gargaɗi da yi wa masu biyayya albishir.
- Wajabcin tsarkake tufafi dan yin sallah, haƙiƙa sun kafa hujja da faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Ka tsarkake tufafinka}.
- Wajabcin yin imani da mala'iku da kuma abin da Allah Ya basu iko a kansa na ayyuka da wasunsu.
Sharhi: العربية
أخبر النبي صلى الله عليه وسلم وهو يحدِّث عن توقُّف الوحي واحتباسه عن النزول في أول بعثته: بينما أنا أمشي في أزقت مكة إذ سمعت صوتًا من السماء، فرفعت بصري، فإذا المَلَك جبريل الذي جاءني بغار حراء جالس على كرسي بين السماء والأرض، فرُعِبْت وفَزعت منه، فرجعت إلى أهلي فقلت: لفُّوني بثوب. فأنزل الله تعالى: {يَا أَيُّهَا المُدَّثِّرُ} المتلفِّف بثوبه، {قُمْ} بالدعوة {فَأَنْذِرْ} وحذِّر مَن لم يؤمن برسالتك. {وَرَبَّكَ} وإلهك المعبود {فَكَبِّرْ} واحمده وعظمه. {وَثِيَابَكَ} وملابسك {فَطَهِّرْ} وخلصها من النجاسات، {وَالرُّجْزَ} بعبادة الأصنام والاوثان {فَاهْجُرْ} واترك، فقَوِيَ الوحيُ بعد ذلك وتكاثر.
- انقطاع الوحي عن النبي صلى الله عليه وسلم يسيرًا بعد نزول قوله عز وجل: {اقْرَأْ}.
- جواز تحدُّث الإنسان بما حصل له من المِحن بعد زوالها، شكرًا لله تعالى.
- أول ما نزل قوله تعالى: {يَا أَيُّهَا الْمُدَّثِّرُ} بعد نزول: {اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ}.
- فضل الله سبحانه وتعالى على نبيه صلى الله عليه وسلم حيث أفاض عليه وحيه دون انقطاع حتى فارق الدنيا.
- وجوب القيام بالدعوة إلى الله تعالى، وإنذار المُعرِضين وتبشير المطيعين.
- وجوب تطهير الثياب للصلاة، وقد استدلوا على ذلك بقوله تعالى: {وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْ}.
- وجوب الإيمان بالملائكة وبما أقدرهم الله عليه من الأعمال وغيرها.