Hadisai

Lallai Allah Ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي يَعْلَى شَدَّادِ بْنِ أَوْسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ اللهَ كَتَبَ الْإِحْسَانَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ، فَإِذَا قَتَلْتُمْ فَأَحْسِنُوا القِتْلَةَ، وَإِذَا ذَبَحْتُمْ فَأَحْسِنُوا الذِّبْحَةَ، وَلْيُحِدَّ أَحَدُكُمْ شَفْرَتَهُ، وَلْيُرِحْ ذَبِيحَتَهُ».

Fassara

Daga Abu Ya'ala Shaddadu ibnu Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lallai Allah Ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu, idan zaku yi kisa to ku kyautata kisan, kuma idan zaku yi yanka to ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙar tasa, don ya hutar da abin yankansa»

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki Ya wajabta mana kyuatayi a kowane abu, kyuatatawa; ita ce jin tsoron Allah a halin dawwama a bautarsa, da kuma yin alheri da kame cuta ga ababen halitta, yana daga wannan kyautatawar a kisa da yanka. Kyautatawa a kisa a lokacin yin ƙisasi: Shi ne ya zaɓi mafi sauƙin hanyoyi, kuma mafi saurinsu a fitar rai ga wanda za'a kashe. Kyautatawa a yanka: Shi ne ya tausasawa dabba ta hanyar wasa abin da za ayi yankan da shi, kuma kada a wasa a gaban abin da za a yanka ɗin, alhali tana kallon abin da za a yi yankan da shi, kuma kada a yanka alhali akwai wasu dabbobin da suke kallon wadda za a yanka.

Fa'idoji

  • Rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - da tausasawarsa ga halitta.
  • Kyautata kisa da yanka: shi ne ya kasance ta fuskar da shari'a ta halatta.
  • Cikar shari'a da tattaruwarta a kan kowane alheri, yana daga cikin hakan jin ƙan dabbobi da tausasawa garesu.
  • Hani daga musla ga mutum bayan kasheshi
  • Haramta dukkanin abin da a cikinsa akwai azabtarwa ga dabbobi.
Sharhi: العربية

يُخبرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أن الله تعالى أوجبَ علينا الإحسانَ في كل الأشياء، والإحسان: هو مراقبة الله على الدوام، في عبادته وفي بذل الخير وكف الأذى عن المخلوقين، ومن ذلك الإحسان في القتل والذبح. فالإحسان في القتل عند القصاص: بأن يختار أسهلَ الطُّرُق وأخَفَّها وأسرعَها زهوقًا للمقتول. والإحسان في الذبح عند الذكاة: بأن يرفق بالبهيمة بإحداد الآلة، وألّا تُحَدَّ أمام الذبيحة وهي تنظر إليها، وألَّا تُذبح وهناك من الماشية ما ينظر إليها.

  • رحمة الله عزّ وجل ولطفه بالخلق.
  • إحسان القتل والذبح بأن يكون على الوجه المشروع.
  • كمال الشريعة واشتمالها على كل خير، ومن ذلك رحمة الحيوان والرفق به.
  • النهي عن المُثْلة بالإنسان بعد قتله.
  • تحريم كل ما فيه تعذيب للحيوان.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari