Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن أبي بَشير الأنصاري رضي الله عنه: أَنَّهُ كَانَ مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي بَعْضِ أَسْفَارِهِ، قَالَ: فَأَرْسَلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَسُولًا -وَالنَّاسُ فِي مَبِيتِهِمْ-: «لَا يَبْقَيَنَّ فِي رَقَبَةِ بَعِيرٍ قِلَادَةٌ مِنْ وَتَرٍ أَوْ قِلَادَةٌ إِلَّا قُطِعَتْ».
Fassara
Daga Abu Bashir mutumin Madina, Allah Ya yarda da shi: Cewa ya kasance tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a wasu tafiye- tafiyansa, ya ce: Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aika a lokacin munane suna wurin baccinsu Kada a bar wuyan wani raƙumi da wani abin wuya na tsirkiya, ko wani abin wuya dai sai an yanke shi.
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance a wata tafiyarsa a lokacin mutane suna wurin baccin su inda suke bacci a bukkokinsu da shemominsu. Sai ya aika wani mutum don ya sami mutane ya umarcesu da yanke kowanne abu da aka rataya a wuyan raƙumi, shin na tsirkiya ne, ko wani abu kamar ƙararrawa ko takalmi, domin sun kasance suna yi musu rataye saboda tsoron kambun baka, sai aka umarce su da su yanke, domin babu abin da take karawa, kuma anfanarwa da cutarwa suna hannun Allah ne Shi kadai.
Fa'idoji
- Haramcin rataya tsirkiya da abin wuya domin janyo amfani ko kuma tunkuɗe cuta domin haka nau'i ne na shirka.
- Sanya abin wuya wanda ba tsarkiya ba, idan ya kasance domin ado ne ko jan dabba ko ɗaureta, to, wannan babu komai.
- Wajibcin hana ɓarna gwargwadon iko
- Wajibcin ɗamfaruwar zuciya da Allah shi kaɗai babu abokin tarayya da shi.
Sharhi: العربية
كان النبيُّ صلى الله عليه وسلم في بعض أسفاره، والناسُ في مكان نومِهم الذي يَبِيْتُون فيه في رِحالِهم وخيامِهم، فأَرْسَلَ شخصًا إلى الناس يأمرهم بِقَطْع القَلَائد التي تُعَلَّق على البعير سواء كانت من الوَتَر -وَتَر القَوْس- أو من غيره كالجَرَس أو النعل، وذلك لأنهم كانوا يُقَلِّدونها حذرًا من العين، فأُمِرُوا بقطعها؛ لأنها لا تَرُدُّ عنهم شيئًا، وأنَّ النفعَ والضرَّ بيد الله وحده لا شريك له.
- تحريم تعليق الأوتار والقلائد لجلب النفع أو دفع الضر؛ لأن ذلك من الشرك.
- ربط القلادة من غير الوتر إذا كان للزينة أو لقيادة الدابة أو لربطها به فلا بأس به.
- وجوب إنكار المنكر بحسب الاستطاعة.
- وجوب تعلق القلب بالله وحده لا شريك له.