Hadisai

To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi a cikin wani dogon hadisi

Rubutun Larabci

قال سعد بن هشام بن عامر -عندما دخل على عائشة رضي الله عنها-: يَا أُمَّ الْمُؤْمِنِينَ، أَنْبِئِينِي عَنْ خُلُقِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَتْ: أَلَسْتَ تَقْرَأُ الْقُرْآنَ؟ قُلْتُ: بَلَى، قَالَتْ: فَإِنَّ خُلُقَ نَبِيِّ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ الْقُرْآنَ.

Fassara

Sa’ad Ɗan Hisham Ɗan Amir ya ce: A Lokacin da ya zo wurin Nana Aisha Allah Ya yarda da ita: Ya uwar Muminai! Ki ba ni bayani kan ɗabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ta ce: A she ba ka kasance kana karanta Alƙur’ani ba ?? Na ce: Ina karantawa, ta ce: To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne.

Sharhi

An tambayi Uwar Muminai A'isha Allah Ya yarda da ita, a kan ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ta amsa, da jawabi gamamme, ta kuma mayar da mai tambayar zuwa Alƙur’ani mai girma wanda ya ƙunshi dukkanin siffofi na kamala, sai ta ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ɗabia’antuwa ne da ɗabi’u na Alƙur’ani, abin da Alƙur’ani ya yi umarni ya yi, kuma abin da Alƙur’ani ya hana ya nisance shi, sai ɗabi’unsa suka kasance aiki da shi da tsayawa inda ya iyakance, da ladabtuwa da ladubansa da ɗaukar izina da misalai da ƙissoshinsa.

Fa'idoji

  • Kwaɗaitarwa a kan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ɗabi’antuwarsa da ɗabi’un Alƙur’ani.
  • Yabon kyawawan ɗabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma sun kasance daga alkukin [hasken] Wahayi suke.
  • Alƙur’ani ne tushen dukkanin kyawawan ɗabi’u.
  • Ɗabi’u a Musulunci sun ƙunshi addini dukkansa, ta hanyar aikata umarni da kuma barin hani.
Sharhi: العربية

سُئِلتْ أمُّ المؤمنين عائشة رضي الله عنها عن خُلُقِ النبيِّ صلى الله عليه وسلم، فأجابتْ بكلمةٍ جامعةٍ، وأحالتْ السائلَ على القرآنِ الكريم الجامع لكلِّ صفات الكمال، فقالت كان صلى الله عليه وسلم يَتَخَلَّقُ بأخلاق القرآن، ما أَمَرَ به القرآنُ قام به، وما نهى عنه القرآن اجتَنَبَه، فكان خُلُقُه العملَ به، والوقوفَ عند حدودِه، والتأدُّب بآدابِه، والاعتبارَ بأمثاله وقصصه.

  • الحثُّ على التأسّي بالنبي صلى الله عليه وسلم في تَخَلُّقِهِ بأخلاق القرآن.
  • مدح أخلاق رسول الله صلى الله عليه وسلم، وأنها كانت من مِشْكَاة الوحي.
  • القرآن مَصدرٌ لكل الأخلاق الكريمة.
  • الأخلاق في الإسلام تشمل الدينَ كلَّه بفعل الأوامر واجتناب النواهي.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari