Hadisai

Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad

Rubutun Larabci

عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «الرَّاحِمُونَ يَرْحَمُهمُ الرَّحمنُ، ارحَمُوا أهلَ الأرضِ يَرْحْمْكُم مَن في السّماء».

Fassara

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa waɗanda suke jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman Yana jin ƙan su da rahamarSa wacce ta yalwaci kowanne abu; don sakayyar da ta dace. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarni da jin ƙan waɗanda ke ƙasa mutum ne, ko dabba, ko tsuntsu, ko waninsa na nau'ikan halitta sakamakon hakan (shi ne) Allah Zai ji kanku daga saman sammanSa.

Fa'idoji

  • Addinin Musulunci addini ne na rahama, shi gabaɗayansa a tsaye yake a kan biyayya ga Allah da kyautatawa zuwa ga halitta.
  • Allah -Mai girma da ɗaukaka - Mai siffantuwa ne da rahama, kuma tsarki ya tabbatar maSa Shi ne Mai rahama a duniya Mai rahama a lahira, Mai sadar da rahama ne ga bayinSa.
  • Sakayya tana daga jinsin aiki, masu jin ƙai Allah Yana jin ƙansu.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ الذين يرحمون غيرَهم يرحمُهم الرحمنُ برحمتِه التي وسعت كلَّ شيء؛ جزاءً وفاقًا. ثم أَمَرَ صلى الله عليه وسلم برحمةِ جميعِ مَن في الأرض مِن إنسانٍ أو حيوانٍ أو طيرٍ أو غيرِه من أنواع الخلق وجزاء ذلك أنْ يرحمَكم الله من فوق سمواته.

  • دين الإسلام دين الرحمة، وهو قائم كله على طاعة الله والإحسان إلى الخلق.
  • الله عز وجل متصف بالرحمة، وهو سبحانه الرحمن الرحيم، مُوْصِلُ الرحمة إلى عباده.
  • الجزاء من جنس العمل، فالراحمون يرحمهم الله.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari