Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «يَقُولُ اللَّهُ تَعَالَى لِأَهْوَنِ أَهْلِ النَّارِ عَذَابًا يَوْمَ القِيَامَةِ: لَوْ أَنَّ لَكَ مَا فِي الأَرْضِ مِنْ شَيْءٍ أَكُنْتَ تَفْتَدِي بِهِ؟ فَيَقُولُ: نَعَمْ، فَيَقُولُ: أَرَدْتُ مِنْكَ أَهْوَنَ مِنْ هَذَا، وَأَنْتَ فِي صُلْبِ آدَمَ: أَلّاَ تُشْرِكَ بِي شَيْئًا، فَأَبَيْتَ إِلَّا أَنْ تُشْرِكَ بِي».
Fassara
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta azaba a ranar lahira: Shin da ace duk abinda ke cikin ƙasa naka ne shin zaka fanshi kanka da shi? Sai ya ce: Eh, Sai ya ce: Na so ƙasa da hakan daga gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam: Kada ka ka yi min tarayya da wani abu, sai kaƙi sai dai ka yi shirka daNi".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta a zaba bayan shigarta: Da ace duniya da abinda ke cikinta nakane shin zaka fanshi kanka da ita daga wannan azabar? Sai ya ce: Eh, Sai Allah Ya ce: Haƙiƙa Na nema daga gareka kuma Na umarceka da mafi sauƙi daga hakan lokacin da aka karɓi alƙawari gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam da kada ka yi shirka daNi da wani abu; sai kaƙi lokacin da Na fitar da kai zuwa duniya sai dai shirka.
Fa'idoji
- Falalar Tauhidi da sauƙin aiki da shi.
- Haɗarin shirka da Allah - Maɗaukakin sarki - da ƙarshenta.
- Allah Ya riƙi alƙawari ga 'ya'yan Adam a bayan babansu Adam da rashin yin shirka.
- GargaɗI akan shirka kuma cewa duniya gabaɗayanta ba zata wadatar da kafiri da komai ba a ranar lahira.
Sharhi: العربية
أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنّ الله تعالى يقول لأهون أهل النار عذابًا بعد دخولها: لو كانت لك الدنيا وما فيها أكنت مُفتديًا بها من هذا العذاب؟ فيقول: نعم، فيقول الله: قد طَلبتُ منك وأمرتُك بأيسر من ذلك حين أُخذ الميثاق عليك وأنت في صُلْبِ آدم ألّا تشرك بي شيئًا؛ فأبيتَ إذْ أخرجتُك إلى الدنيا إلا الشرك.
- فضل التوحيد ويُسْر العمل به.
- خطر الشرك بالله تعالى وعاقبته.
- أخذ الله الميثاق على بني آدم وهم في ظَهْر أبيهم آدم بعدم الشرك.
- التحذير من الشرك وأنّ الدنيا كلَّها لا تغني عن الكافر يوم القيامة شيئًا.