Hadisai

Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَن أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ أَدْنَى مَقْعَدِ أَحَدِكُمْ مِنَ الْجَنَّةِ أَنْ يَقُولَ لَهُ: تَمَنَّ فَيَتَمَنَّى، وَيَتَمَنَّى، فَيَقُولُ لَهُ: هَلْ تَمَنَّيْتَ؟ فَيَقُولُ: نَعَمْ، فَيَقُولُ لَهُ: فَإِنَّ لَكَ مَا تَمَنَّيْتَ وَمِثْلَهُ مَعَهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce : «Lallai mafi ƙankantar matsayin ɗayanku a cikin aljanna shi ne Ya ce masa: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, sai Ya ce da shi: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce da shi: Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi ƙanƙantar matsayi da daraja ga wanda ya shiga aljanna shi ne Ya ce da shi: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, har sai ya zama babu wani burin da zai rage masa sai ya ambace shi , sai Ya ce masa: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce masa: To lallai kana da abinda ka yi burin dama kwatankwacinsa tare da shi.

Fa'idoji

  • Fifikon matsayin 'yan aljanna.
  • Bayanin girman karamcin Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.
  • Ni'imar aljanna ba ta taƙaituwa akan wani ayyanannen abu, kai mumini zai samu dukkan abinda yake burinsa kuma ransa yake sha'awarsa dan falala da kyauta da kuma karamci daga Allah - Maɗaukakin sarki -.
Sharhi: العربية

أخبر النبيُّ صلى الله عليه وسلم أن أدنى وأقل منزلة ومرتبة لمن دخل الجنة أن يقول له: تمن، فيتمنى، ويتمنى، حتى لا يبقى له أمنية إلا وذكرها، فيقول له: هل تمنيت؟ فيقول: نعم، فيقول له: فإن لك ما تمنيت ومثله معه.

  • تفاوت منازل أهل الجنة.
  • بيان عظم كرم الله سبحانه وتعالى.
  • لا ينحصر نعيم الجنة على شيء معين، بل يجد فيها المؤمن كل ما يتمناه وتشتهيه نفسه فضلًا وجودًا وكرمًا من عند الله تعالى.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari