Hadisai

Idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, ya ce: Allah -Maɗaukakin sarki - zai ce: Kuna son wani abu ne da zan ƙaro muku shi?

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ صُهَيْبٍ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِذَا دَخَلَ أَهْلُ الْجَنَّةِ الْجَنَّةَ، قَالَ: يَقُولُ اللهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: تُرِيدُونَ شَيْئًا أَزِيدُكُمْ؟ فَيَقُولُونَ: أَلَمْ تُبَيِّضْ وُجُوهَنَا؟ أَلَمْ تُدْخِلْنَا الْجَنَّةَ، وَتُنَجِّنَا مِنَ النَّارِ؟ قَالَ: فَيَكْشِفُ الْحِجَابَ، فَمَا أُعْطُوا شَيْئًا أَحَبَّ إِلَيْهِمْ مِنَ النَّظَرِ إِلَى رَبِّهِمْ عَزَّ وَجَلَّ».

Fassara

Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, ya ce: Allah -Maɗaukakin sarki - zai ce: Kuna son wani abu ne da zan ƙaro muku shi? sai su ce: Ba Ka haskaka fusokinmu ba? kuma ba Ka shigar da mu aljannah ba, kuma Ka tseratar da mu daga wuta? ya ce: Sai a yaye hijabi, ba'a basu wani abu mafi soyuwa a gare su ba daga duba zuwa Ubanginsu - Mai girma da ɗaukaka -".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - zai ce musu: Shin kuna son wani abu da zan ƙaro muku? Sai 'yan aljanna gaba ɗayansu su ce: Shin baKa hasakaka fuskokinmu ba? Shin baKa shigar da mu aljanna ba, kuma Ka tseratar damu daga wuta? Sai Allah Ya gusar da shamaki kuma Ya ɗauke shi; hijabinSa (shi ne) haske, ba'a basu wani abuba mafi soyuwa garesu daga duba zuwa Ubangijinsu - Mai girma da ɗaukaka ba.

Fa'idoji

  • Yaye hijabi daga 'yan aljanna sai su ga Ubangijinsu, amma kafirai; to su ababen haramtawa ne daga ganin Ubangiji.
  • Mafi girman ni'imar aljanna (ita ce) ganin muminai ga Ubangijinsu.
  • Dukkan 'yan aljanna duk yadda matsayinsu ya saɓa zasu ga Ubangijinsu - Maɗaukaki -.
  • Falalar Allah ga muminai da shigar da su aljanna.
  • Muhimmancin gaggawa zuwa aljanna da ayyuka na gari da bin Allah - Maɗaukakin sarki - da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Sharhi: العربية

يُخْبِرُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّه إذا دَخَلَ أهلُ الجَنةِ الجنةَ، يقول الله تبارك وتعالى لهم: هل تُريدون شيئًا أَزِيْدُكم؟ فيقول أهلُ الجنة كلُّهم: ألم تُبَيِّضْ وجوهَنا؟ ألم تدخلنا الجنة، وتنجِنا من النار؟ فيُزيلُ الله الحِجَابَ ويَرفعه؛ وحِجَابُه النُّور، فما أُعْطوا شيئًا أحبَّ إليهم من النَّظَر إلى ربِّهم عز وجل.

  • كَشْفُ الحِجاب عن أهلِ الجَنة فيَرَون ربَّهم، وأما الكفار؛ فمَحْرُومون منها.
  • أعظمُ نعيم الجنة رؤيةُ المؤمنين لربهم.
  • كلُّ أهل الجنة مهما اختلفت منازلُهم سيرون ربَّهم جل وعلا.
  • فضل الله على المؤمنين بإدخالهم الجنة.
  • أهمية المسارعة إلى الجنة بالأعمال الصالحة وطاعة الله تعالى ورسوله صلى الله عليه وسلم.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari