Hadisai

Lallai a cikin aljanna akwai wata kasuwar da 'yan aljanna suke zuwanta kowacce Jumu'a

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ فِي الْجَنَّةِ لَسُوقًا، يَأْتُونَهَا كُلَّ جُمُعَةٍ، فَتَهُبُّ رِيحُ الشَّمَالِ فَتَحْثُو فِي وُجُوهِهِمْ وَثِيَابِهِمْ، فَيَزْدَادُونَ حُسْنًا وَجَمَالًا، فَيَرْجِعُونَ إِلَى أَهْلِيهِمْ وَقَدِ ازْدَادُوا حُسْنًا وَجَمَالًا، فَيَقُولُ لَهُمْ أَهْلُوهُمْ: وَاللهِ لَقَدِ ازْدَدْتُمْ بَعْدَنَا حُسْنًا وَجَمَالًا، فَيَقُولُونَ: وَأَنْتُمْ وَاللهِ لَقَدِ ازْدَدْتُمْ بَعْدَنَا حُسْنًا وَجَمَالًا».

Fassara

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai a cikin aljanna akwai wata kasuwar da 'yan aljanna suke zuwanta kowacce Jumu'a, sai iskar arewa ta taso sai ta watsu a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa. sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ado, sai iyalansu suce musu: Wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ado a bayanmu".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljanna akwai wani wurin da zasu dinga taruwa a wurin, babu siye da siyarwa a cikinsa suna ɗaukar abinda suke so daga gare shi, suna zuwa wurin gwargwdan kwana bakwai, sai iskar arewa ta taso, sai ta motsa a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa, sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ƙawa, sai iyalansu su ce musu: Wallahi haƙiƙa a bayanmu kun ƙara kyau da ƙawa, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu.

Fa'idoji

  • Bayanin cewa 'yan aljanna suna samun ƙaruwar kyau da ƙawa.
  • Hadisan suna sawa mutum kwaɗayi a cikin aiki nagari wanda ake taka shi zuwa wannan gidan.
  • An keɓanci iskar arewa da ambato ne; domin cewa ita ta kasance mafi kyan iska a wurin larabawa yayin da take zuwa da alheri da kuma ruwa.
  • Kwaɗaitarwa akan kira zuwa ga Allah ta hanyar kwaɗaitar da aljanna da kuma ni'imarta.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن في الجنة مكانًا يجتمعون فيه، ليس فيه بيع ولا شراء يأخذون منه ما أرادوا، يأتونه مقدار كل سبعة أيام، فتهب ريح الشمال، فتحرك في وجوههم وثيابهم، فيزدادون حسنًا وجمالًا، فيرجعون إلى أهليهم وقد ازدادوا حسنًا وجمالًا، فيقول لهم أهلوهم: والله لقد ازددتم بعدنا حُسنًا وجمالًا، فيقولون: وأنتم والله لقد ازددتم بعدنا حسنًا وجمالًا.

  • بيان أن أهل الجنة في زيادة حُسن وجمال.
  • الأحاديث توجب للإنسان الرغبة في العمل الصالح الذي يتوصّل به إلى هذه الدار.
  • خص ريح الشمال بالذكر؛ لأنها كانت أحسن الرياح عند العرب حيث كانت تأتي بالخير والمطر.
  • الحث على الدعوة إلى الله بالترغيب بالجنة ونعيمها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari