Hadisai

Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) gurin farce a kan ƙafafunsa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi (wurin) sai ya ce: "Koma ka kyautata alwalarka" Sai ya dawo, sannan ya yi sallah

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce ne a baki dayan ruwayoyin saMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه قال: أَخْبَرَنِي عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ: أَنَّ رَجُلًا تَوَضَّأَ فَتَرَكَ مَوْضِعَ ظُفُرٍ عَلَى قَدَمِهِ فَأَبْصَرَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «ارْجِعْ فَأَحْسِنْ وُضُوءَكَ» فَرَجَعَ، ثُمَّ صَلَّى.

Fassara

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Umar Dan Alkhaddab ya bani labari: Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) gurin farce a kan ƙafafunsa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi (wurin) sai ya ce: "Koma ka kyautata alwalarka" Sai ya dawo, sannan ya yi sallah.

Sharhi

Umar - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya gama alwalarsa, sai ya bar gwargwadan farce a ƙafarsa (Lam’a) ruwa bai same shi ba, sai ya ce masa yana mai nuni zuwa gurin da bai sami ruwa ba: Ka koma ka kyautata alwalarka ka cikata ka ba wa kowacce gaba haƙƙinta na ruwa. Sai mutumin ya koma ya cika alwalarsa, sannan ya yi sallah.

Fa'idoji

  • Wajabcin gaggawa zuwa horo da aikin alheri, da fadakar da wanda bai sani ba da rafkananne, musamman ma idan barnar ta kasance lalacewar ibadarsa za ta kasance akan akan barnar.
  • Wajabcin game gabban alwala da ruwa, kuma cewa wanda ya bar wani yanki daga gaba - koda ƙarami ne - alwala ba ta ingantuwa daga gare shi, kuma sakewa ce ta wajaba idan ya jima kafin ya gani.
  • Halaccin kyautata alwala, hakan ta hanyar cikata da kyautata akan yadda aka yi umarni da ita a shari'ance.
  • Kafafuwa biyu suna daga gabban alwala, kuma shafa ba ta isuwa a cikinsu, kawai babu makawa sai an wanke su.
  • Jerantawa, yana kamata tsakanin gabban alwala, ta yadda zai wanke kowacce gaba kafin ta gabaninta ta bushe.
  • Rashin sani da mantuwa ba sa sarayar da wajibi, kawai suna sarayar da zunubi ne, wannan mutumin wanda bai kyautata alwalarsa ba saboda rashin sani, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi bai sarayar masa da wajibi ba, wato alwala, kawai ya umarce shi ya saketa.
Sharhi: العربية

أَخْبَرَ عُمَرُ رضي الله عنه أنَّ النبيَّ صلى الله عليه وسلم أَبْصَرَ رَجلًا انتهى مِن وضوئه، فتَرَكَ قَدْرَ ظُفرٍ في قَدَمه لم يُصِبْهُ ماءُ الوضوء، فقال له مشيرًا إلى موضع التقصير: ارجع فأحسن وضوءك وأَتِمَّه وأعْطِ كلَّ عُضوٍ حقَّه من الماء، فرجع الرجل فأتمّ وضوءه ثم صلى.

  • وجوبُ المبَادَرة إلى الأمرِ بالمعروف، وإرشادِ الجاهلِ والغَافل، وخصوصًا إذا كان المُنكَر يترتَّب عليه فسادُ عبادته.
  • وجوب تعميم أعضاء الوضوء بالماء، وأنَّ من ترك جزءًا من العضو -ولو يسيرًا- لم يصحّ معه الوضوء ولزمته الإعادة إذا كان الفاصل طويلًا.
  • مشروعية إحسان الوضوء، وذلك بإتمامه وإسْبَاغه على الوجه المأمور به شرعًا.
  • القدمان من أعضاء الوضوء، ولا يكفي فيهما المسح، بل لابدَّ من الغسل.
  • ينبغي الموالاة بين أعضاء الوضوء، بحيث يَغسل كلَّ عضو قبل أن يَجِفَّ الذي قبله.
  • الجهل والنسيان لا يُسقِطان الواجبَ، وإنما يُسقِطان الإثمَ، فهذا الرجل الذي لم يُسْبِغ وضوءه لجهله لم يُسقِط عنه النبيُّ صلى الله عليه وسلم الواجبَ، وهو الوضوء، وإنما أمره أن يعيدَه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari