Hadisai

Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي ذَرٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «لاَ يَرْمِي رَجُلٌ رَجُلًا بِالفُسُوقِ، وَلاَ يَرْمِيهِ بِالكُفْرِ، إِلَّا ارْتَدَّتْ عَلَيْهِ، إِنْ لَمْ يَكُنْ صَاحِبُهُ كَذَلِكَ».

Fassara

Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi cewa wanda ya cewa wani: Kai fasiƙine, ko: Kai kafiri ne, idan ya kasance bai zama kamar yadda ya faɗa ba, ya kasance shi ne wanda ya cancanci siffar da aka anbata kuma maganarsa ta dawo masa, amma idan ya kasance kamar yadda ya faɗa wani abu ba zai dawo masa ba; saboda kasancewarsa ya yi gaskiya a abinda ya faɗa.

Fa'idoji

  • Haramcin jifan mutane da kafirci ko fasiƙanci, ba tare da wani abin halattawa na shari'a ba.
  • Wajabcin neman tabbaci a fitar da hukunce-hukunce akan mutane.
  • Ibnu Daƙiƙul Id ya ce: Wannan narko ne mai girma ga wanda ya kafirta wani daga musulmai alhali bai zama kamar hakan ba, kuma ita matsala ce mai girma.
  • Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Sai dai ba ya lazimtar kasancewarsa bai zamo fasiƙi ko kafiri ba da hakan, a ce kuma ba zai zama mai saɓo a surar faɗinsa gare shi ba: Kai fasiƙi ne, kai a wannan surar (akwai) rarrabewa: Idan ya yi nufin yi masa nasiha ko nasihar waninsa da bayanin halinsa to ya halatta, idan ya yi nufin aibanta shi da yayata shi da hakan da tsantsar cutarsa to bai halatta ba; domin cewa shi abin umarta ne da rufa masa asiri da sanar da shi da yi masa wa'azi da kyakkyawa, a duk lokacin da hakan ya yi wu gare shi da sauƙi to ba ya halatta gare shi ya aikata shi da tsanani; domin cewa shi zai iya kasancewa sababi na ruɗar da shi da kuma zarcewarsa akan wannan aikin, kamar yadda yake a dabi'ar da yawa daga mutane ita ce tsanani, musamman ma idan mai umarnin ya kasance bai kai wanda ake umartar a daraja ba.
Sharhi: العربية

حَذَّرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنّ مَن قال لآخر: أنت فاسق، أو: أنت كافر، فإنْ كان ليس كما قال، كان هو المُستَحِق للوصف المذكور ورَجَعَ عليه قولُه، وأما إذا كان كما قال لم يرجع عليه شيء؛ لكونه صدق فيما قال.

  • تحريم رمي الناس بالكفر أو الفسق، بغير مُسَوِّغ شرعي.
  • وجوب التثبُّت في إصدار الأحكام على الناس.
  • قال ابن دقيق العيد: وهذا وعيد عظيم لمن أكفر أحدًا من المسلمين وليس كذلك، وهي ورطة عظيمة.
  • قال ابن حجر العسقلاني: ولكن لا يلزم من كونه لا يصير بذلك فاسقًا ولا كافرًا أن لا يكون آثمًا في صورة قوله له: أنت فاسق، بل في هذه الصورة تفصيل: إن قَصَدَ نُصْحَه أو نُصْحَ غيرِه بِبَيان حاله جاز، وإن قَصَدَ تَعْيِيْرَه وشُهرَتَه بذلك ومَحْضَ أذاه لم يجز؛ لأنه مأمور بالستر عليه وتعليمه وعِظَتِه بالحسنى، فمهما أمكنه ذلك بالرفق لا يجوز له أن يفعله بالعُنْف؛ لأنه قد يكون سببًا لإغرائه وإصراره على ذلك الفعل كما في طَبْعِ كثير من الناس من الأَنَفَة، ولا سيّما إن كان الآمِرُ دونَ المأمورِ في المنزلة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari