Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ سَمُرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَحْلِفُوا بِالطَّوَاغِي، وَلَا بِآبَائِكُمْ».
Fassara
Daga Abdurrahman ɗan Samura - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku yi rantsuwa da ɗagutai, ko da iyayenku".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga rantsuwa da ɗawagitai, jam'ine na dagutu, sune gumakan da mushrikai suke bauta musu koma bayan Allah, sune sababin shisshiginsu da kafircinsu, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin hani daga rantsuwa da iyaye; inda ya kasance daga al'adar larabawa a Jahiliyya shi ne su yi rantsuwa da iyayensu dan alfahari da girmamawa.
Fa'idoji
- Rantsuwa bata halatta sai da Allah da sunayenSa da siffofinSa.
- Haramcin rantsuwa da ɗawagitai, da kuma iyaye da shugabanni da gumaka, da abinda ke kama da su daga dukkan ƙarya.
- Rantsuwa da wanin Allah yana daga ƙaramar shirka, takan iya zama shirka babba, idan akwai girmama wanda aka yi rantsuwa da shi a cikin zuciya, kuma shi yana girma shi kamar yadda yake girmama Allah, ko cewa shi yana ƙudirce wani abu a cikinsa na bauta.
Sharhi: العربية
يَنْهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم عن الحَلِف بالطواغي، جمع طاغية، وهي الأصنام التي كان المشركون يَعبدونها مِن دون الله، وهي سببُ طغيانِهم وكفرِهم، وينهى صلى الله عليه وسلم عن الحلف بالآباء؛ حيث كان من عادة العرب في الجاهلية أن يَحلفوا بآبائهم افتخارًا وتعظيمًا.
- الحَلف لا يجوز إلا بالله وأسمائه وصفاته.
- تحريم الحلف بالطواغيت، والآباء والرؤساء والأصنام، وما شابَهَها من كل باطل.
- الحلف بغير الله من الشرك الأصغر، وقد يكون شركًا أكبر، إذا قام بقلبه تعظيم المحلوف به وأنه يعظِّمه كما يعظِّم الله أو أنه يعتقد فيه شيئًا من العبادة.