Hadisai

Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neAbu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad

Rubutun Larabci

عَنْ بُرَيْدَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ حَلَفَ بِالْأَمَانَةِ فَلَيْسَ مِنَّا».

Fassara

Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani kuma ya gargaɗar daga rantsuwa da amana, kuma cewa wanda ya aikata hakan to ba shi daga cikinmu.

Fa'idoji

  • Haramcin rantsuwa da wanin Allah - Maɗaukakin sarki -, kuma daga cikin hakan: amana, kuma hakan yana daga ƙaramar shirka.
  • Amana ta ƙunshi ɗa'a da bauta da ajiya da bayarwa hannu da hannu da amintarwa.
  • Rantsuwa bata ƙulluwa sai da Allah - Maɗaukakin sarki - ko da wani suna daga sunayenSa ko wata siffa daga siffofinSa.
  • AlKhaɗɗabi ya ce: Wannan yana kama da karhancin ya zama saboda cewa shi ya yi umarni a yi rantsuwa da Allah ne da kuma siffofinSa, amana kuwa ba ta daga siffofinSa, kawai ita wani al'amari ce daga aumarninSa, kuma farilla ce daga farillanSa, sai aka hanasu su rantse da ita dan abinda ke cikin hakan na daidaitawa tsakaninta da tsakanin sunayen Allah - Mai girma da ɗaukaka - da kuma siffofinSa.
Sharhi: العربية

نَهَى النبيُّ صلى الله عليه وسلم وحَذَّرَ مِن الحَلِف بالأمانة، وأنَّ مَن فَعل ذلك فليس منا.

  • تَحريم الحَلِف بغير الله تعالى، ومنه: الحلف بالأمانة، وأنه من الشرك الأصغر.
  • الأمانة تَشمل الطاعة والعبادة والوديعة والنقد والأمان.
  • اليمين لا تنعقد إلا بالله تعالى أو باسم من أسمائه أو بصفة من صفاته.
  • قال الخطابي: هذا يشبه أن تكون الكراهة فيه من أجل أنه أَمَرَ أَن يحلف بالله وبصفاته، وليست الأمانة من صفاته، وإنما هي أَمْرٌ من أَمْرِه، وفَرْض من فروضه، فنُهوا عنه لما في ذلك من التسوية بينها وبين أسماء الله عز وجل وصفاته.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari