النحل

An-Nahl

ayoyi 128MakkiyaJuzu'i 14

Mahmoud Khalil Al-HussaryHafsu daga Asim - Murattal

Saitunan karatu

Jagorar launukan tajwidi

Sunaye, misalai da layukan ƙasa iri-iri suna bayyana ƙa'idojin baya ga launi. An ɗauko misalan daga rubutun Alƙur'ani da aka wallafa.

Gunna
وَمِمَّا2:3
Nau'o'in Ikhfa'i
يُنفِقُونَ2:3
Nau'o'in Idgami
هُدًى لِّلْمُتَّقِينَ2:2
Iƙlabi
أَلِيمٌۢ بِمَا2:10
Ƙalƙala
رَزَقْنَـٰهُمْ2:3
Madda: harka 2
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Madda: harka 2, 4 ko 6
ٱلرَّحِيمِ1:1
Madda: harka 4 ko 5
بِمَآ2:4
Madda: harka 6
ٱلضَّآلِّينَ1:7
Hamzatul wasli
ٱللَّهِ1:1
Lam Shamsiyya
ٱلرَّحْمَـٰنِ1:1
Haruffan da ba a furtawa
ٱلصَّلَوٰةَ2:3

Alamomin tajwidi: cpfair/quran-tajweed (CC BY 4.0), an gina su daga ReciteQuran.com da mus'hafan tajwidi na Dar al-Maarifah; an daidaita wurarensu da rubutun Tanzil na yanzu.

Fassarar Hausa - Abubakar Gumi. Siga: 1.2.2. Sabuntawa ta ƙarshe: 2025-06-26. QuranEnc.com

  1. 8

    وَٱلْخَيْلَ وَٱلْبِغَالَ وَٱلْحَمِيرَ لِتَرْكَبُوهَا وَزِينَةً ۚ وَيَخْلُقُ مَا لَا تَعْلَمُونَ

    Kuma da dawãki[1] da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba.

    Bayanan ƙasan shafi

    [1] Haɗa dawãki da alfadarai zuwa ga jãkuna kuma aka ce dõmin "hawansu da yin ƙawã" yana nũna cewa ba a cin dawãki da alfadarai dõmin an san cewa an hana cin jãkuna a lõkacin yãƙin Khaibara, kuma ãyõyin da ke gaba da wannan ãya sun nũna anã cin dabbõbin ni'ima kuma anã hawansu, kuma cin nãma yã fi hawa zama ni'ima, sabõda haka, shĩ ne ya kamãta a ambata inda ya halatta. Wannan ne mazhabar Mãliki da Ahu Hanĩfa, kuma shĩ ne maganar Abdullah bn Abbãs Allah Ya yarda da su. Wasu sun ce ana cin dawãki da alfadarai dõmin cewa, "Anã hawansu dõmin ƙawa," bã ya hana a yi wani abu da su, wato cin nãmansu, dõmin a cikin Bukhãri daMuslim an ruwaito halaccin cin dawãki. Wannan shĩ ne maganar Al-Hasan da Shuraih da 'Aɗa' a da Sa'ĩd bn Jubair. Kuma Shi ne mazhabar shãfi'i da Is'hãƙ. Sun yi hujja da halaccin nãman dawãki da abin da Asmã'u bint Abĩ Bakar Assiddiƙ ta ce, "Mun sõke wata gõɗiya' muka ci a zamanin Manzon Allah,a Madina." Kuma a cikin Bukhãri da Muslim daga jãbir, Allah Ya yarda da shi, "Mun ci dawãki da jãkunan jeji a Khaibara, kuma Annabi tsira da aminci sun tabbata a gare shi, ya hana jãkunan gida" Acikin Abĩ Dãwud, "Mun yanke dawãki da alfadarai da jakuna alhãli yunwa ta kãmã mu, amma sai Annabi ya hana mu cin jãkuna da alfadarai, bai hana mu cin dawãki ba" Nĩ, a ganina, ra'ayin cin dawãki ya fi ƙarfi dõmin sũrar ta sauka a Makka, amma hadisin yankan gõɗiyar, a Madĩna aka yi shi. Saboda haka surar ba ta shãfe shi ba. Dũbi Radd Al-Azhãn.

    Tafsirin As-Sa'di (Larabci)

    Ya ƙunshi ayoyi 8

    {8} {والخيلَ والبغالَ والحميرَ}: سخَّرناها لكم؛ {لتَرْكَبوها وزينةً}؛ أي: تارة تستعملونها للضرورة في الركوب، وتارة لأجل الجمال والزينة، ولم يذكر الأكل؛ لأنَّ البغال والحمير محرَّم أكلها، والخيل لا تستعمل في الغالب للأكل، بل يُنهى عن ذبحها لأجل الأكل خوفاً من انقطاعها، وإلاَّ؛ فقد ثبت في «الصحيحين» أنَّ النبيَّ - صلى الله عليه وسلم - أذن في لحوم الخيل. {ويخلق ما لا تعلمونَ}: مما يكون بعد نزول القرآن من الأشياء التي يركبها الخلقُ في البَرِّ والبحرِ والجوِّ ويستعملونها في منافعهم ومصالحهم؛ فإنَّه لم يذكُرْها بأعيانها؛ لأنَّ الله تعالى لم يذكر في كتابه إلا ما يعرفُهُ العباد أو يعرفون نظيرَه، وأمَّا ما ليس له نظيرٌ؛ فإنَّه لو ذُكِرَ؛ لم يعرِفوه ولم يفهموا المراد منه، فيَذْكُرُ أصلاً جامعاً يدخُلُ فيه ما يعلمون وما لا يعلمون؛ كما ذكر نعيم الجنة، وسمَّى منه ما نعلم ونشاهد نظيره؛ كالنخل والأعناب، والرمَّان وأجمل ما لا نعرف له نظيراً في قوله: {فيهما من كلِّ فاكهةٍ زوجانِ}؛ فكذلك هنا ذكر ما نعرفه من المراكب؛ كالخيل والبغال والحمير والإبل والسفن، وأجمل الباقي في قوله: {ويَخْلُقُ ما لا تعلمون}.

    Tafsirin As-Sa'di, Larabci v1.0.0, QuranEnc.com

    Zaɓuɓɓukan aya
    Buɗe shafin ayar 8 Duba karatuna: Na gwaji
    Rubutun sirri

Tafsiri

Sura ta gabaAl-Isra'iالإسراء

Ba da rahoton kuskure

Ƙari