Hadisai

Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَن أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا بَالُ أَقْوَامٍ يَرْفَعُونَ أَبْصَارَهُمْ إِلَى السَّمَاءِ فِي صَلاَتِهِمْ»، فَاشْتَدَّ قَوْلُهُ فِي ذَلِكَ، حَتَّى قَالَ: «لَيَنْتَهُنَّ عَنْ ذَلِكَ أَوْ لَتُخْطَفَنَّ أَبْصَارُهُمْ».

Fassara

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Meke damun wasu mutane ne suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallarsu". Sai maganrasa ta yi tsanani a kan hakan, har ya ce: "Kodai su hanu daga hakan ko a fauce magannansu".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗi waɗanda suke ɗaga idanuwansu zuwa sama a cikin sallah a lokacin addu'a ko waninta, sannan tsawatarwarsa ta yi tsanani da narkonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wanda ya aikata haka da cewa shi yana jin tsoro akan idanuwansu kada a fauce musu su a karɓesu da gaggawa ta inda basa ji sai kawai ga shi sun rasa n'imar gani.

Fa'idoji

  • Kyakkyawan tsarin Da'awar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da bayanin gaskiya; domin shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bayyana wanda ya saɓa ba; domin abin nufi shi ne bayanin gaskiya alhali kuwa ta tabbata; domin kuma a cikinsa akwai suturtawa ga mai saɓawa kuma ya fi sa a karɓa.
  • Hani mai ƙarfi, da narko mai tsanani akan wanda ya ɗaga ganinsa zuwa sama a cikin sallah.
  • Ya faɗa a cikin Aunil Ma'abud: Illa a cikin hakan cewa shi idan ya ɗaga ganinsa zuwa sama to ya fita daga saitin alƙibla kuma ya bijire mata dama siffar sallar.
  • Ɗaga ido zuwa sama yana kore Khushu'i a cikin sallah.
  • Girman sha'anin sallah, kuma yana wajaba akan mai sallah ya kasance a cikinta akan cikar ladabi tare da Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
Sharhi: العربية

حذَّر النبي صلى الله عليه وسلم الذين يرفعون أبصارهم إلى السماء في الصلاة عند الدعاء أو غيره، ثم اشتد زَجْرُه وتوعُّدُه صلى الله عليه وسلم على من يفعل ذلك بأنه يخشى على أبصارهم أن تُخطف منهم وتؤخذ بسرعة بحيث لا يشعرون إلا وقد فَقَدوا نِعمة البَصر.

  • حُسن دعوة النبي صلى الله عليه وسلم وبيان الحق؛ لأنه صلى الله عليه وسلم لم يَكشف عن المُخالف؛ لأن المقصود بيان الحقِّ وقد حصل؛ ولأن فيه سَترًا على المخالف وأدعى للقبول.
  • النَّهي الأكيد، والوعيد الشَّديد على من رفع بَصره إلى السماء في الصلاة.
  • قال في عون المعبود: والعلة في ذلك أنه إذا رفع بصره إلى السماء خرج عن سمت القبلة وأعرض عنها وعن هيئة الصلاة.
  • منافاة رفع البصر للخشوع في الصلاة.
  • عِظَم شأن الصلاة، وأنه يجب على المُصلِّي أن يكون فيها على كمال الأدب مع الله عز وجل.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari