Hadisai

Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَن الحَسَنِ قال: حَدَّثنا جُنْدَبُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنه، فِي هَذَا المَسْجِدِ، وَمَا نَسِينَا مُنْذُ حَدَّثَنَا، وَمَا نَخْشَى أَنْ يَكُونَ جُنْدُبٌ كَذَبَ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلّى الله عليه وسلم: «كَانَ فِيمَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ رَجُلٌ بِهِ جُرْحٌ، فَجَزِعَ، فَأَخَذَ سِكِّينًا فَحَزَّ بِهَا يَدَهُ، فَمَا رَقَأَ الدَّمُ حَتَّى مَاتَ، قَالَ اللَّهُ تَعَالَى: بَادَرَنِي عَبْدِي بِنَفْسِهِ، حَرَّمْتُ عَلَيْهِ الجَنَّةَ».

Fassara

Daga Hassan ya ce: Jundub ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya yi mana hadisi a cikin wannan masallacin, kuma bamu manta ba tun da ya yi mana hadisin, kuma bama jin tsoron cewa Jundub ya yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninku ya kasance rauni ya same shi, sai ya kasa haƙuri bai yi haƙuri akan raɗaɗin ba, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa da ita kuma ya gaggautowa mutuwa, jinin bai tsaya ba har ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Bawa Na ya yi miNi gaggawa da ransa, haƙiƙa na haramta masa aljanna.

Fa'idoji

  • Falalar haƙuri akan jarrabawa, da barin ƙorafi saboda raɗaɗi dan kar ya kai zuwa mafi tsanani daga gare shi.
  • Bayar da bayanin al'ummun da suka shuɗe da abinda a cikinsa akwai alheri da kuma wa'azi.
  • Ibnu Hajar ya ce: A cikinsa akwai tsayuwa a wurin haƙƙoƙin Allah da kuma rahamarSa ga halittarSa inda Ya haramta musu kashe rayukansu, kuma cewa rayuka mallakin Allah ne.
  • Haramta aikata sabubban da zasu kai zuwa kashe rai, da kuma narko mai tsanani a cikin hakan.
  • Ibnu Hajar ya ce: Hakan ya yi nuni akan ya yanke hannun ne dan nufin mutuwa ba dan nufin yin maganin da yake kyakkyawan zai yi anfani da shi ba.
Sharhi: العربية

أخبر النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنه كان فيمن كان قبلنا رجل أصابه جرح، فجزع ولم يصبر على الألم، فأخذ سكينًا فقطع بها يده واستعجل الموت، فما انقطع الدم حتى مات، قال الله تعالى: بادرني عبدي بنفسه، قد حرمت عليه الجنة.

  • فضيلة الصبر على البلاء، وترك التضجر من الآلام لئلا يُفْضِي إلى أشد منها.
  • التحديث عن الأمم الماضية بما فيه الخير والعظة.
  • قال ابن حجر: فيه الوقوف عند حقوق الله ورحمته بخلقه حيث حَرّم عليهم قتل نفوسهم وأن الأنفس ملك الله.
  • تحريم تعاطي الأسباب المفضية إلى قتل النفس، والوعيد الشديد في ذلك.
  • قال ابن حجر: ودل ذلك على أنه حزَّها لإرادة الموت لا لقصد المداواة التي يغلب على الظن الانتفاع بها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari