Hadisai

Ban taɓa ganin ma'abocin gashin kai ba mafi kyau a cikin kayan ado jajaye (mayafi da kwarjalle saƙar Yaman) kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنِ الْبَرَاءِ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: مَا رَأَيْتُ مِنْ ذِي لِمَّةٍ أَحْسَنَ فِي حُلَّةٍ حَمْرَاءَ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، شَعْرُهُ يَضْرِبُ مَنْكِبَيْهِ، بَعِيدَ مَا بَيْنَ الْمَنْكِبَيْنِ، لَيْسَ بِالطَّوِيلِ وَلَا بِالْقَصِيرِ.

Fassara

Daga Bara’u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ban taɓa ganin ma'abocin gashin kai ba mafi kyau a cikin kayan ado jajaye (mayafi da kwarjalle saƙar Yaman) kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - gashinsa yana taɓa kafaɗunsa, mai nisan abinda ke tsakanin kafaɗu ne, shi ba dogo ba ne ba kuma gajere ba ne.

Sharhi

Bara’u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi bai taɓa ganin wani mai gashi ba, wanda gashin kansa mai tsawo ne ya kai kafaɗu, kuma yana sanya mayafi da kwarjalle baƙaƙe alhali a cikinsa akwai zanen ja mafi kyau kamar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba -, ya kasance daga cikin siffofinsa na halitta shi mai nisan abinda ke tsakanin kafaɗu ne, mai yalwar ƙirji, kuma ya kasance mai tsakatsakiyar daidaituwa tsakanin tsawo da gajarta.

Fa'idoji

  • Bayanin wasu daga cikin siffofin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - masu kyau a zahiri na kyawun gashi da faɗin ƙirji, da kyawun daidaituwa, da makamancin haka.
  • Son sahabbai masu girma - Allah Ya yarda da su - ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, har cewa su suna hakaitowa kuma suna ruwaito ɗabi'unsa da siffofinsa na jiki da kuma na ma'ana ga na bayansu.
Sharhi: العربية

يخبر البراء بن عازب رضي الله عنه أنه ما رأى أحدًا شَعَرُ رأسِه طويل قد وَصَل إلى منكبيه، ويلبس إزارًا ورداءً أسود وفيه خطوط حمراء أحسن من رسول الله صلى الله عليه وسلم، وأن من صفته الخَلْقية أنه كان بعيدَ ما بين المنكبين، واسع الصدر، وكان متوسط القَامَة بين الطويل والقصير.

  • بيان بعض صفات النبي صلى الله عليه وسلم الجميلة في الظاهر من حسن الشعر ورَحَابة الصدر، وحسن القامة، وغير ذلك.
  • محبة الصحابة الكرام رضي الله عنهم للنبي صلى الله عليه وسلم، حتى أنهم يحكون وينقلون لمن بعدهم شمائله وأوصافه الجسدية والمعنوية.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari