Hadisai

Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عن عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «الْكَبَائِرُ: الْإِشْرَاكُ بِاللهِ، وَعُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ، وَقَتْلُ النَّفْسِ، وَالْيَمِينُ الْغَمُوسُ».

Fassara

Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana manyan zunubai cewa su ne waɗanda aka yi narko (alƙawarin azaba) a kan wanda ya aikata su da narko mai tsanani a duniya ko a lahira. Na farkonsu "Yi wa Allah shirka": Shi ne karkatar da kowanne nau'i daga Nau’ukan ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah cikin abin da ya keɓanci Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa. Na biyunsu: "Saɓawa iyaye": Shi ne dukkanin abin da yake nuna cutarwa ga iyaye; magana ce ko aiki, da barin kyautata musu. Na ukunsu "Kashe rai": ba tare da wani haƙƙi ba, kamar kisa a kan zalunci da ta'addanci. Na huɗunsu "Rantsuwa mai dulmiyarwa": Ita ce rantsuwa alhali yana mai ƙarya yana sane cewa ƙarya yake, an ambaceta da hakan; domin cewa tana dulmiya mai yinta a laifi sannan a wuta.

Fa'idoji

  • Rantsuwa mai dulmiyarwa ba ta da kaffara; don tsananin haɗarinta da girmanta, kawai dai akwai [damar] tuba a cikinta.
  • Taƙaituwa a kan ambaton waɗannan manyan laifukan guda huɗu a hadisin [ya kasance] don girman laifinsu ne, ba don su ne kadai ba.
  • Zunubai sun kasu zuwa manya da ƙanana, babban laifi shi ne: Dukkanin zunubin da a cikinsa akwai uƙuba ta duniya, kamar haddi da tsinuwa, ko narko na lahira, kamar narko da shiga wuta, kuma manyan zunubai hawa-hawa ne wasu sun fi wasu muni a haramci. Kananan zunubai su ne waɗanda ba waɗannan ba.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم كبائر الذنوب، وهي التي تُوُعِّدَ فاعلُها بوعيد شديد في الدنيا أو الآخرة. فأوَّلُها "الإِشرَاكُ بِالله": وهو صَرْفُ أيِّ نوع من أنواع العبادة لغير الله، وتسوية غير الله بالله فيما هو من خصائص الله في ألوهيته وربوبيته وأسمائه وصفاته. وثانيها "عُقُوقُ الوَالِدَينِ": وهو كلُّ ما يوجب الأذى للأبوين قولًا كان أو فعلًا، وترك الإحسان إليهما. وثالثها "قَتْل النَّفْس": بغير حق، كالقتل ظلمًا وعدوانًا. ورابعها "اليَمِين الغَمُوسُ": وهي الحلف كاذبًا على علم منه بكذبه، سميت بذلك؛ لأنَّها تَغْمِسُ صاحبَها في الإِثم أو في النار.

  • اليمين الغموس لا كفارة لها؛ لشدة خطرها وجرمها، وإنما فيها التوبة.
  • الاقتصار على ذكر هذه الكبائر الأربع في الحديث لعظيم إثمها، وليس لحصرها.
  • الذنوب تنقسم إلى كبائر وصغائر، والكبيرة هي: كلُّ ذنب فيه عقوبة دنيوية، كالحدود واللعن، أو وعيد أُخروي، كالوعيد بدخول النار، وأن الكبائر دركات بعضها أغلظ من بعض في التحريم، وصغائر الذنوب هي ما سوى الكبائر.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari