Hadisai

Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ السَّاعَةِ، فَقَالَ: مَتَى السَّاعَةُ؟ قَالَ: «وَمَاذَا أَعْدَدْتَ لَهَا». قَالَ: لاَ شَيْءَ، إِلَّا أَنِّي أُحِبُّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «أَنْتَ مَعَ مَنْ أَحْبَبْتَ». قَالَ أَنَسٌ: فَمَا فَرِحْنَا بِشَيْءٍ، فَرِحْنَا بِقَوْلِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَنْتَ مَعَ مَنْ أَحْبَبْتَ» قَالَ أَنَسٌ: فَأَنَا أُحِبُّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَبَا بَكْرٍ، وَعُمَرَ، وَأَرْجُو أَنْ أَكُونَ مَعَهُمْ بِحُبِّي إِيَّاهُمْ، وَإِنْ لَمْ أَعْمَلْ بِمِثْلِ أَعْمَالِهِمْ.

Fassara

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?" Ya ce: Babu komai, sai dai ni ina son Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce; "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Bamu taba farin ciki da wani abu ba, irin farin cikinmu da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Ni ina son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma ina kaunar in kasance tare da su dan son da nake musu, koda ban yi aiki irin aikinsu ba.

Sharhi

Wani mutumin karkara irin waɗanda suke zama a sahara ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: game da lokacin tashin alkiyama? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Meka tanadar mata na aiki na gari? Sai mai tambayar ya ce: Ban tanadi wani aiki mai yawa ba sai dai ni ina son Allah da ManzonSa, bai ambaci wanin hakan ba daga ayyuaka na zuciya da jiki da dukiya; domin su dukkaninsu rassa ne ga soyayya masu jerantuwa ne akanta, kuma domin soyayya ta gaskiya tana zaburar da kokarin yin aiki na gari. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Lallai kai kana tare da wanda ka so a aljanna. Sai sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka yi farin ciki mai girma da wannan busharar. Sannan Anas ya bada labarin cewa shi yana son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma yana kaunar ya kasance tare da su, koda aikinsa bai zama irin aikinsu ba.

Fa'idoji

  • Hikimar Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - a amsawa mai tambaya, yayin da ya nunar da shi akan abinda zai himmatu akansa kuma zai tseratar da shi, shi ne: Yin tanadi dan lahira da abinda zai anfanar da kuma aiki na gari.
  • Allah Ya boye sanin alkiyama ga bayi dan mutum ya kasance mai tanadi mai shirin haɗuwa da Allah.
  • Falalar son Allah da ManzonSa da mutanen kirki cikin muminai, da gargaɗarwa daga son mushrikai.
  • Faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Kai kana tare da wanda ka so. Ba ana nufin daidaituwa a daraja da matsayi ba, a'a abin nufi kasancewarsu a aljanna ta inda kowane ɗaya daga cikinsu zai samu damar ganin ɗayan koda guri ya nisanta.
  • Fadakar da musulmi dan shagaltuwa da mafi maslaha da kuma mafi anfani gare shi, da barin tambaya daga abinda ba zai anfanar da shi ba.
Sharhi: العربية

سَألَ النبيَّ صلى الله عليه وسلم رجلٌ أعرابيٌّ مِمّن يَسكن الصحراء: عن وقت قيام الساعة؟ فقال له صلى الله عليه وسلم: وما أعددتَ لها من العمل الصالح؟ فقال السائل: ما أعددتُ لها كبيرَ عملٍ إلا أني أحبُّ اللهَ ورسولَه، ولم يذكر غيرَها من العبادات القلبية والبدنية والمالية؛ لأنها كلُّها فروع للمحبة مترتبة عليها، ولأن المحبة الصادقة باعثة للاجتهاد في العمل الصالح. فقال له صلى الله عليه وسلم: إنك مع مَن أحببتَ في الجنة. ففرح أصحابُ النبيِّ صلى الله عليه وسلم بهذه البشرى فرحًا شديدًا. ثم أَخبرَ أنسٌ رضي الله عنه أنه يحب النبي صلى الله عليه وسلم وأبا بكر، وعمر، ويرجو أن يكون معهم، وإن كان عملُه ليس مثلَ عملِهم.

  • حكمة رسول الله صلى الله عليه وسلم في إجابة السائل، حيث دلَّه على الذي يهمه وينجيه، وهو: الاستعداد للآخرة بما ينفع والعمل الصالح.
  • أخفى اللهُ علمَ الساعة على العباد ليبقى المرء مستعدًّا متجهزًا للقاء الله.
  • فضل محبة الله ورسوله والصالحين من المؤمنين، والتحذير من محبة المشركين.
  • قوله صلى الله عليه وسلم: أنت مع من أحببت. ليس المراد التساوي في الدرجة والمنزلة، بل المراد كونهم في الجنة بحيث يتمكَّن كل واحد منهم من رؤية الآخر وإن بَعُد المكان.
  • توجيه المسلم للانشغال بالأصلح والأنفع له، وترك السؤال عما لا ينفعه.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari