Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عن عَائِشَةَ رضيَ الله عنها قالت: إِنِّي سمعْتُ رسولَ الله صلى الله عليه وسلم يقول: «لَا صَلَاةَ بِحَضْرَةِ الطَّعَامِ، وَلَا هُوَ يُدَافِعُهُ الْأَخْبَثَانِ».
Fassara
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida).
Sharhi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana sallah in a wurin akwai abincin da ran mai sallah yake sha'awarsa, kuma zuciyarsa take rataye da shi. Haka nan ya hana sallah tare da matse najasa biyu - su ne fitsari da bahaya -, saboda shagaltuwa da matse najasar.
Fa'idoji
- Ya kamata ga mai sallah ya nisantar da dukkanin abin da zai shagaltar da shi a cikin sallarsa kafin ya shiga cikin sallar.
Sharhi: العربية
نَهى رسولُ الله صلى الله عليه وسلم عن الصلاة بحضور الطعام الذي تَتُوْقُ نَفسُ المُصلي إليه، ويَتعلق قلبُه به. وكذلك نهى عن الصلاة مع مدافعة الأخبثين -وهما البول والغائط--، لانشغاله بمدافعة الأذى.
- ينبغي للمصلي إبعاد كلِّ ما يَشْغَلُه في صلاته قبل الدخول فيها.