Hadisai

Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi zance mara anfani

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عن أبِي هُرَيرةَ رضي الله عنه أنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلمَ قال: «إذا قُلْتَ لِصَاحِبِكَ: أَنْصِتْ، يومَ الجمعةِ، والْإِمامُ يَخْطُبُ، فَقَدْ لَغَوْتَ».

Fassara

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi zance mara anfani".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa daga ladubba na wajibi ga wanda ya halarci huɗubar Juma'a: Shi ne yin ahieu ga mai huɗuba; don ya yi tuntuntuni cikin wa'azin, kuma wanda ya yi magana - ko da da ƙanƙanin abu ne - alhali liman yana huɗuba, sai ya ce wa waninsa: "Ka yi shiru" ka "saurara", to, haƙiƙa falalar sallar Juma'a ta wuce shi.

Fa'idoji

  • Haramta zance alokacin jin huɗuba, ko da da hani ne daga abin ƙi, ko amsa sallama da gaishe da mai atishawa.
  • An togance wanda yake yi wa liman magana, ko liman yake yi masa magana [daga wannan hanin].
  • Halaccin yin magana a lokacin huɗubobi biyu a yayin buƙata.
  • Idan an ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali liman yana huɗuba, to, za ka yi masa salati, a ɓoye, haka nan cewa amin ga addu'a.
Sharhi: العربية

يُبَيِّنُ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ مِن الآداب الواجبة لِمَن حَضَرَ خطبةَ الجمعة: الإنصاتَ للخطيب؛ ليتدبَّر المواعظ، وأنَّ مَن تَكَلَّمَ -ولو بأقلِّ شيء- والإمام يخطب، فقال لغيره: "اسكت" و"استمع"، فقد فاته فَضْلُ صلاةِ الجمعة.

  • تحريم الكلام حال سماع الخطبة، ولو بالنهي عن المنكر أو ردِّ السلام وتشميت العاطس.
  • يُستثنى مِن هذا مَن يخاطِبُ الإمامَ أو يُخاطِبُهُ الإمامُ.
  • جواز الكلام بين الخطبتين عند الحاجة.
  • إذا ذُكِرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم والإمامُ يَخطب فإنك تُصلي عليه وتُسلِّم سِرًّا، وكذلك التأمين على الدعاء.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari