Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أُمِّ عَطِيَّةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: نُهِينَا عَنِ اتِّبَاعِ الجَنَائِزِ، وَلَمْ يُعْزَمْ عَلَيْنَا.
Fassara
Daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce: An hanamu bin jana'iza, amma ba'a ƙarfafa hanin a kanmu ba.
Sharhi
Ummu Aɗiyya al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana mata bin jana'iza; hakan saboda abinda ake jin tsoro a cikin hakan na fitina garesu da kuma fitinuwa da su, da kuma ƙarancin haƙurinsu, sannan Allah Ya yarda da ita ta bada labarin cewa bai ƙarfafa hanin ba kamar yadda yake aikatawa a sauran abubuwan da ya hana.
Fa'idoji
- Hana mata bin jana'iza, kuma hakan mai gamewa ne a binta zuwa inda ake shirya gawar da kuma yi mata sallah, da kuma zuwa maƙabarta inda za'a rufeta.
- dalilin hanin shi ne mata ba sa iya ganin irin waɗannan guraren masu baƙanta rai da kuma abubuwa masu tasiri; wataƙila fishi da rashin haƙuri akan abinda zai kore haƙuri na wajibi ya bayyana daga garesu.
- Asali a cikin hanin shi ne haramci, saidai cewa Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta fahimta ta hanyar alamar hali cewa hanasu bin jana'izar da aka yi ba a yanke yake ba, kuma ba mai ƙarfi ba ne, saidai haƙiƙa wasu hadisan sun zo mafi yawa daga abinda suke nuni akan tsananin bin jana'iza sama daga abinda wannan hadisin yake nuni a kansa.
Sharhi: العربية
تخبر أم عطية الأنصارية رضي الله عنها أن النبي صلى الله عليه وسلم نهى النساء عن المشي مع الجنائز؛ وذلك لما يُخشى في ذلك من الفتنة لهن وبهن، وقلّة صبرهن، ثم أخبرت رضي الله عنها أن النبي صلى الله عليه وسلم لم يؤكد في المنع كما يفعل في سائر المنهيات.
- نهي النساء عن اتباع الجنائز، وهو عام في اتباعها إلى حيث تجهز ويصلى عليها، وإلى المقبرة حيث تدفن.
- علة النهي أن النساء لا يُطِقْن مثل هذه المشاهد المحزنة والمواقف المؤثرة؛ فربما ظهر منهن من التسخط والجزع ما ينافي الصبر الواجب.
- الأصل في النهي التحريم إلا أن أم عطية رضي الله عنها فهمت من قرينة الحال أن نهيهن عن اتباع الجنائز ليس جازمًا مؤكَّدًا، لكن قد وردت أحاديث أدلّ على التشديد في اتباع الجنائز أكثر مما يدل عليه هذا الحديث.