Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِذَا رَأَى أَحَدُكُمُ الرُّؤْيَا يُحِبُّهَا فَإِنَّهَا مِنَ اللَّهِ، فَلْيَحْمَدِ اللَّهَ عَلَيْهَا وَلْيُحَدِّثْ بِهَا، وَإِذَا رَأَى غَيْرَ ذَلِكَ مِمَّا يَكْرَهُ، فَإِنَّمَا هِيَ مِنَ الشَّيْطَانِ، فَلْيَسْتَعِذْ مِنْ شَرِّهَا، وَلاَ يَذْكُرْهَا لِأَحَدٍ، فَإِنَّهَا لَنْ تَضُرَّهُ».
Fassara
Daga Abu Sa'id Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, kuma ya nunar da cewa ya godewa Allah akansa, ya kuma bada labarinsa, idan kuma ya ga abinda yake ƙinsa yake baƙanta masa rai to shi kawai daga Shaiɗan ne; to ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, kada ya faɗawa kowa; (to mafarkin) ba zai cutar da shi ba , inda Allah Ya sanya abinda aka ambata sababi na kuɓuta daga abinda yake na mugun mafarkin .
Fa'idoji
- Rabe-raben mafarki: 1- Kyakkyawan mafarki, shi ne mafarki na gaskiya kuma bushara daga Allah da (mutum) yake ganinsa ko agane masa, 2- Zancen zuci shi ne abinda mutum yake zantar da kansa a farke, 3- Baƙantawa da tsoratarwar Shaiɗan da razanarwa daga gare shi dan ya baƙanta ran ɗan Adam ne.
- Abinda aka ambata a taƙaice a Babin kyakkyawan mafarki abubuwa ne uku: Shi ne ya godewa Allah akansa, kuma ya yi albushir da shi, kuma ya faɗawa wanda yake so shi banda wanda yake ƙinsa.
- Abinda aka ambata a taƙaice daga ladabin mummunan mafarki abubuwa ne guda biyar: Ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, da kuma sharrin Shaiɗan, kuma ya yi tofi a hagunsa sau uku lokacin da ya farka daga baccinsa, kuma kada ya faɗawa kowa mafarkin, idan ya yi nufin komawa baccinsa to ya juya daga ɓangaren da yake akansa; to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba.
- Ibnu Hajar ya ce: Hikima a cikinsa cewa shi idan ya fadawa wanda ba ya ƙauna kyakkyawan mafarki zai iya fassara masa da abinda ba ya so kodai dan ƙiyayya ko dan hassada, kuma zai iya faruwa akan waccan siffar ko ya gaggautowa kansa baƙin ciki da takaici daga hakan, to sai aka umarce shi da barin fadawa wanda ba ya so saboda hakan.
- Godiya a yayin faruwar ni'imomi, da sabuntuwar abubuwan buri, to hakan sababi ne na dawwamar su.
Sharhi: العربية
أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ الرؤيا الصالحةَ المُفرِحة في المنام من الله، وأرشد بأنْ يَحمد الله عليها، ويخبر بها، وإذا رأى ما يَكره ويُحزن فإنما هي من الشيطان؛ فليستعذ بالله من شرها، ولا يذكرها لأحد؛ فإنها لا تضره حيث جعل الله ما ذُكر سببًا للسلامة من المكروه المترتِّب على الرؤيا.
- أقسام الرؤيا: 1- الرؤيا الصالحة، وهي رؤيا حق وبشرى من الله يراها أو تُرى له، 2- حديث النفس وهي ما يحدِّث بها الرجل نفسه في اليقظة، 3- تحزين وتخويف الشيطان وأهاويل منه ليحزن ابن آدم.
- حاصل ما ذكر من أبواب الرؤيا الصالحة ثلاثة أشياء: أن يحمد الله عليها، وأن يستبشر بها، وأن يتحدث بها لكن لمن يحب دون من يكره.
- حاصل ما ذكر من أدب الرؤيا المكروهة خمسة أشياء: أن يتعوَّذ بالله من شرها، ومن شر الشيطان، وأن يتفل حين يهب من نومه عن يساره ثلاثا، ولا يذكرها لأحد أصلًا، وإذا أراد أن يرجع لنومه يتحوّل عن جنبه الذي كان عليه؛ فإنها لا تضره.
- قال ابن حجر: الحكمة فيه أنه إذا حدَّث بالرؤيا الحسنة من لا يحب قد يفسِّرها له بما لا يحب إما بُغضًا وإما حسدًا، فقد تقع على تلك الصفة أو يتعجّل لنفسه من ذلك حُزنًا ونكدًا، فأمر بترك تحديث مَن لا يُحِب بسبب ذلك.
- الحمد عند حدوث النِّعَم، وتجدد المنن، فذلك سبب لدوامها.