Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0
Rubutun Larabci
عَنْ عُبَادَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ شَهِدَ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، وَأَنَّ عِيسَى عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ وَكَلِمَتُهُ أَلْقَاهَا إِلَى مَرْيَمَ وَرُوحٌ مِنْهُ، وَالْجَنَّةُ حَقٌّ، وَالنَّارُ حَقٌّ، أَدْخَلَهُ اللهُ الْجَنَّةَ عَلَى مَا كَانَ مِنَ الْعَمَلِ».
Fassara
Daga Ubada - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne kalmarSa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare Shi, kuma aljanna gaskiya ce haka wuta ma gaskiya ce, Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa".
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bamu labarin cewa wanda ya furta kalmar tauhidi yana masanin ma'anarta yana mai aiki da abinda ta hukunta, ya kuma shaida da ubudiyyar Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma manzancinsa, ya kuma yarda da kasantuwar Annabi Isa bawa ne na Allah da kuma manzancinsa, kuma cewa Allah Ya halicce shi da fadinSa "Ka sance" sai ya kasance , kuma cewa shi ruhi ne daga rayukan Allah wadanda Allah Ya haliccesu, ya kuma barrantar da babarsa daga abinda yahudawa suke jingina mata, ya yi imani da cewa aljanna gaskiya ce, kuma wuta gaskiya ce, yana mai kudirce samuwarsu, kuma cewa su ni'imar Allah ne da azabarSa, kuma ya mutu a kan hakan, to makomarsa tana aljanna koda ya kasance ya gajiya ne a ayyukan da'a, kuma yana da zunubai.
Fa'idoji
- Allah - Madaukakin sarki - Ya halicci Annabi Isa dan Maryam da kalmar (kasan ce) ba tare da uba ba.
- Hadawa tsakanin kasancewar Annabi Isa da Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare su - bayin Allah ne kuma manzanninSa ne, su biyun Manzannin ne ba'a karyata su, kuma bayi ne (ga Allah) ba'a bauta musu.
- Falalar tauhidi da kankarewarsa ga zunubai, kuma cewa makomar mai tauhidi ita ce aljanna koda wasu zunubai sun afka masa.
Sharhi: العربية
يُخْبِرُنا رسولُ الله صلى الله عليه وسلم أنَّ مَن نَطَقَ بكلمةِ التوحيد عارفًا لمعناها عاملًا بمقتضاها، وشهد بعبودية محمد صلى الله عليه وسلم ورسالته، واعترف بعبودية عيسى ورسالته، وأنَّ الله خلقه بقوله "كن" فكان، وأنه روح من الأرواح التي خلقها الله، وَبَرَّأَ أُمَّهُ مِمّا نَسَبَه إليها اليهود، وآمن بأن الجنة حق، وأن النار حق، معتقدًا وجودهما، وأنهما نعيم الله وعذابه، ومات على ذلك؛ فمصيره إلى الجنة وإن كان مقصِّرًا في الطاعات، وله ذنوب.
- الله تعالى خَلَقَ عيسى ابن مريم بكلمة (كُنْ) من غير أب.
- الجمع بين كون عيسى ومحمد صلى الله عليهما وسلم عبدي الله ورسوليه، فهما رسولان لا يكذبان، وعبدان لا يُعْبَدان.
- فضل التوحيد وتكفيره للذنوب، وأنَّ مصيرَ الموحِّد الجنةُ وإنْ وقع منه بعض الذنوب.