Hadisai

Na kasance ina wanka ni da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya (abin wanka) daya mu duka biyun muna da janaba, ya kasance yana umartata, sai insa gwafso, sai ya rungumeni alhali ni ina al’ada,

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤمنينَ رضي الله عنها قَالَتْ: كُنْتُ أَغْتَسِلُ أَنَا وَالنَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ إِنَاءٍ وَاحِدٍ كِلاَنَا جُنُبٌ، وَكَانَ يَأْمُرُنِي، فَأَتَّزِرُ، فَيُبَاشِرُنِي وَأَنَا حَائِضٌ، وَكَانَ يُخْرِجُ رَأْسَهُ إِلَيَّ وَهُوَ مُعْتَكِفٌ فَأَغْسِلُهُ وَأَنَا حَائِضٌ.

Fassara

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Na kasance ina wanka ni da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya (abin wanka) daya mu duka biyun muna da janaba, ya kasance yana umartata, sai insa gwafso, sai ya rungumeni alhali ni ina al’ada, ya kasance yana fito min da kansa alhali shi yana i'itikafi sai in wanke masa shi alhali ina al’ada.

Sharhi

Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da sashin halayenta na musamman tare da shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, daga hakan: Ta kasance tana wankan janaba tare da shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- daga kwarya daya sai su dinga diban ruwan tare. Kuma cewa shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi idan ya yi nufin zuwa mata alhali tana al’ada sai ya umarceta ta rufe jikinta daga cibiya zuwa gwiwa, sai ya rungumeta da abinda ke koma bayan jima'i. Kuma cewa shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana i'itikafi a cikin masallaci sai ya fitar da kansa ga Nana A'isha alhali tana cikin dakinta tana al’ada.

Fa'idoji

  • Halaccin wankan mutum da matarsa a kwarya daya.
  • Halaccin rungumar mai al’ada a abinda ke kasa da farji, kuma cewa jikinta mai tsarki ne.
  • An so sanyawarta gwafso a lokacin rungumemeniya.
  • Rikon sabubba masu hana afkawa cikin haram.
  • Hana mai al’ada zama a cikin masallaci.
  • Halaccin tabawarta abubuwa danyu da busassu, daga hakan (akwai) wanke gashi da tsefe shi.
  • Kyakkyawan mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga iyalansa.
Sharhi: العربية

أَخْبَرَتْ عائشةُ أُمُّ المؤمنين رضي الله عنها عن بعض أحوالِها الخاصة معه صلى الله عليه وسلم، ومن ذلك: أنها كانت تغتسل من الجنابة معه صلى الله عليه وسلم مِن إناءٍ واحدٍ فيأخذان منه معًا. وأنه صلى الله عليه وسلم إذا أراد إتيانَها وهي حائض أَمَرَها أَنْ تُغطي بدنَها مِن السُّرَّةِ إلى الركبة، فيباشرها بما دون الجماع. وأنه صلى الله عليه وسلم كان يَعتكف في المسجد فيُخرِج رأسَه إلى عائشة فتغسله وهي في بيتها حائضٌ.

  • جواز اغتسال الرجل وزوجتِه مِن إناءٍ واحد.
  • جواز مباشرة الحائض فيما دون الفرج، وأنَّ بدنَها طاهر.
  • استحباب لبسِها الإزارَ وقتَ المباشرة.
  • اتخاذ الأسباب المانعة من الوقوع في المحرم.
  • منع مُكْثِ الحائضِ في المسجد.
  • إباحة مباشرتِها الأشياءَ رطبة أو يابسة، ومن ذلك غسل الشعر وترجيله.
  • حسن عشرة النبي صلى الله عليه وسلم لأهله.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari