Hadisai

Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا مِنْ نَبِيٍّ بَعَثَهُ اللهُ فِي أُمَّةٍ قَبْلِي إِلَّا كَانَ لَهُ مِنْ أُمَّتِهِ حَوَارِيُّونَ، وَأَصْحَابٌ يَأْخُذُونَ بِسُنَّتِهِ وَيَقْتَدُونَ بِأَمْرِهِ، ثُمَّ إِنَّهَا تَخْلُفُ مِنْ بَعْدِهِمْ خُلُوفٌ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ، وَيَفْعَلُونَ مَا لَا يُؤْمَرُونَ، فَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِيَدِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِلِسَانِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِقَلْبِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَلَيْسَ وَرَاءَ ذَلِكَ مِنَ الْإِيمَانِ حَبَّةُ خَرْدَلٍ».

Fassara

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi, sannan wasu masu sabawa zasu saba a bayansu suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umarce su ba, wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi muminin ne, kuma babu wani kwatankwacin kwayar komayya na imani bayan hakan".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a wata al'umma kafin shi sai ya kasance yana da tsarkakakku da mataimaka da mayaka masu ikhlasi a cikin al'ummarsa, wadanda suka cancanci kalifanci a bayansa; suna riko da sunnarsa, kuma suna koyi da umarninsa, sannan wasu mutane zasu zo bayan wadancan magabata na garin wadanda babu alheri a cikinsu; suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umartarsu; wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi muminin ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi mumini ne, kuma babu wani imani kwatankwacin kwayar komayya bayan hakan.

Fa'idoji

  • Kwadaitarwa akan yakar masu sabawa shari'a da maganganunsu da kuma ayyukansu.
  • Rashin yin inkari a zuciya dalili ne akan raunin imani ko tafiyarsa.
  • Sawwakewar Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ga Annabwa ga wanda zai dauki sakonsu a bayansu.
  • Wanda yake son tsira to ya wajaba ya bi tafarkin Annabawa; domin duk wata hanyar da ba hanyarsu ba to halaka ce kuma bata ce.
  • Duk lokacin da zamani ya nisanta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - sai mutane su bar sunnoni kuma su bi soye-soyen zukatansu, kuma su farar da bidi'o'i.
  • Bayanin matakan jihadi, cewa shi da hannu ne ga wanda zai iya canzawa, kamar shuwagabanni da mahukunta da sarakai, haka kuma da magana yana kasancewa ne ta hanyar bayyana gaskiya da kira zuwa gareta, haka kuma da zuciya yana kasancewa ne ta hanyar yin inkarin abin ki da rashin sonsa ko yarda da shi.
  • Wajabcin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki.
Sharhi: العربية

أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنه ما مِن نبيٍّ بعثَه الله في أمة قَبلَه إلا كان له مِن أمته أصفياء وأنصار ومجاهدون مخلصون، يَصْلحون للخِلافة بعده؛ يأخذون بِسنّته، ويقتدون بأمره، ثم يجيء بعد أولئك السلف الصالح أُناسٌ لا خيرَ فيهم؛ يقولون ما لا يفعلون، ويفعلون ما لا يؤمرون؛ فمَن جاهدَهم بيده فهو مؤمن، ومن جاهدهم بلسانه فهو مؤمن، ومن جاهدهم بقلبه فهو مؤمن، وليس وراء ذلك من الإيمان حَبَّةُ خَرْدَلٍ.

  • الحث على مجاهدة المخالفين للشرع بأقوالهم وأفعالهم.
  • عدم إنكار القلب للمنكر دليلٌ على ضَعْفِ الإيمان أو ذَهابِه.
  • تيسير الله سبحانه وتعالى للأنبياء مَن يَحمِلُ رسالتَهم مِن بعدِهم.
  • مَن أراد النجاة فعليه باتباع منهج الأنبياء؛ لأنَّ كل طريق سوى طريقهم هلاك وغواية.
  • كلَّما بَعُد العهدُ مِن النبي صلى الله عليه وسلم وأصحابه رضي الله عنهم تَرَكَ الناس السُّنَنَ واتبعوا الأهواءَ وأَحَدَثُوا البِدَع.
  • بيان مراتب الجهاد، وأنه باليد لمن يستطيع التغيير، كأولياء الأمور والحكَّام والأمراء، وبالقول يكون ببيان الحق والدعوة إليه، وبالقلب يكون بإنكار المنكر وعدم حُبِّه أو الرضا به.
  • وجوب الأمر بالمعروف والنهي عن المنكر.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari