Hadisai

‌Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neMuslim ne ya rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الدُّنْيَا سِجْنُ الْمُؤْمِنِ وَجَنَّةُ الْكَافِرِ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce».

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa rayuwar duniya ga mumini kamar kurkuku ce dan wajibci ga abubuwan da shari'a da aka ɗora masa, na aikata abinda aka yi umarni da shi da kuma barin abinda aka yi gargaɗi da shi, idan ya mutu ya huta daga wannan kuma zai koma zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi masa tanadi na ni'ima madawwamiya. ita (duniyar) kamar kuma aljanna ce ga kafiri; domin cewa shi yana aikata dukkanin abinda ransa yake sha'awarsa kuma son ransa yake umartarsa, idan ya mutu zai juya zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yimasa tanadi a ranar alƙiyama na azaba tabbatacciya.

Fa'idoji

  • Nawawi ya ce: Dukkan mumini abin sawa a cikin kurkuku ne abin hana wa sha'awowin da aka haramta da waɗanda aka karhanta a duniya ne, kuma abin ɗorawa ayyukan ɗa'a ne masu wahala, idan ya mutu ya huta daga wannan, kuma ya koma zuwa ga abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi masa tanadi na ni'ima madawwamiya, da kuma hutu tsarkakakke daga tawaya. Amma kafiri kawai yana da abinda ya samu a duniya tare da ƙarancinsa da kuma gurɓatarsa da abubuwan da suke ɓata su, idan ya mutu zai tafi zuwa ga azaba madawwamiya, da kuma taɓewa ta har abada.
  • Sindi ya ce: Faɗinsa: (Kurkukun mumini ce) cewa shi koda ya kasance a cikin ni'ima to aljanna ce mafi alheri gare shi, (Kuma aljannar kafiri ce) cewa shi ko da ya kasance a cikin wahala to wuta ita ce mafi sharri ce gare shi.
  • Wulaƙantar duniya ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
  • Duniya gidan jarraba ce ga masu imani.
  • Kafiri an gaggauto da aljannarsa a duniyarsa; sai aka yi masa uƙuba da haramta aljannar lahira da kuma ni'imarta.
Sharhi: العربية

أخبر النبي صلى الله عليه وسلم أن الحياة الدنيا للمؤمن كالسجن لالتزامه بالتكاليف الشرعية من فعل المأمور وترك المحذور، فإذا مات استراح من هذا وانقلب إلى ما أعد الله تعالى له من النعيم الدائم، وهي للكافر كالجنة؛ لأنه يفعل فيها كل ما تشتهيه نفسه ويأمره به هواه، فإذا مات انقلب إلى ما أعد الله تعالى له يوم القيامة من العذاب المقيم.

  • قال النووي: كل مؤمن مسجون ممنوع في الدنيا من الشهوات المحرمة والمكروهة، مكلف بفعل الطاعات الشاقة، فإذا مات استراح من هذا، وانقلب إلى ما أعد الله تعالى له من النعيم الدائم، والراحة الخالصة من النقصان، وأما الكافر فإنما له من ذلك ما حصل في الدنيا مع قلته وتكديره بالمنغصات، فإذا مات صار إلى العذاب الدائم، وشقاء الأبد.
  • قال السندي: قوله (سجن المؤمن) فإنه وإن كان في نعمة فالجنة خير له منها، (وجنة الكافر) فإنه وإن كان في مقيتة فالنار شر له منها.
  • هوان الدنيا على الله تعالى.
  • الدنيا دار ابتلاء وامتحان لأهل الإيمان.
  • الكافر استعجل جنته في دنياه؛ فعوقب بحرمان جنة الآخرة ونعيمها.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari