Hadisai

Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَقُولُ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ: أَنَا عِنْدَ ظَنِّ عَبْدِي، وَأَنَا مَعَهُ حِينَ يَذْكُرُنِي، فَإِنْ ذَكَرَنِي فِي نَفْسِهِ ذَكَرْتُهُ فِي نَفْسِي، وَإِنْ ذَكَرَنِي فِي مَلَإٍ ذَكَرْتُهُ فِي مَلَإٍ خَيْرٍ مِنْهُ، وَإِنِ اقْتَرَبَ إِلَيَّ شِبْرًا، تَقَرَّبْتُ إِلَيْهِ ذِرَاعًا، وَإِنِ اقْتَرَبَ إِلَيَّ ذِرَاعًا، اقْتَرَبْتُ إِلَيْهِ بَاعًا، وَإِنْ أَتَانِي يَمْشِي أَتَيْتُهُ هَرْوَلَةً».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa gareNi yake, zan yi mu'amala da bawaNa gwargwadan zatansa da Ni, hakan dan ƙauna da burin rangwami, kuma Ina yi masa abinda yake tinanin afkuwarsa daga gareNi na alheri ne ko wanin hakan; kuma Ni ina tare da shi da rahama da dacewa da shiriya da kiyayewa da ƙarfafawa idan ya anbaceNi. Idan ya anbaceNi a cikin ransa shi kaɗai a kaɗaice da tasbihi da hailala ko waninsu; zan anbace shi a cikin raiNa. Idan ya anbaceNi a cikin jama'a; zan ambace shi a cikin jama'ar da tafisu yawa kuma ta fisu tsarki. Wanda ya nemi kusanci zuwa ga Allah gwargwadan taki Allah Zai yi masa ƙari sai Ya kusanto zuwa gare shi da zira'i. Idan ya nemi kusanci zuwa gare shi gwargwadan zira'i zai kusanto zuwa gare shi gwargwadan awon faɗin hannaye. Idan ya zo zuwa ga Allah yana tafiya to Allah zai zo masa Yana sassarfa. Bawa idan ya nemi kusanci zuwa ga Ubangijinsa da biyayya gareShi da fuskantowa gareShi, to lallai Ubangiji - Maɗaukakin sarki - Zai ƙara kusanci zuwa gareshi dan sakamako daga jinsin aikinsa. A duk lokacin da bautar mumini ta cika ga Ubangijinsa to Allah Maɗaukakin sarki zai kusanto zuwa gare shi, kyautar Allah da sakamakonSa (ita ce ) mafi yawa daga aikin bawa da kuma wahalarsa, a taƙaice cewa sakamakon Allah mai rinjaya ne akan aiki ta hanyar kaifiyya da kuma kimmiya. Mumini yana kyautata zato, kuma yana aiki, yana gaggawa yana ƙarawa har ya gamu da Allah.

Fa'idoji

  • Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu keɓance-keɓancen AlƘur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninSa, kamar bauta da karanta shi, da yin tsarki sabo da shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
  • Al-Aajurri ya ce: Lallai ma'abota gaskiya suna siffanta Allah - Mai girma da ɗaukaka - da abinda Ya siffanta kanSa - Mai girma da ɗaukaka - da shi, da kuma abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta shi da shi, kuma da abinda sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka siffantaShi da shi, wannan (ita ce) mazhabar malamai daga waɗanda ya bi bai yi ƙirƙire ba, Ya ƙare. Ahlus Sunna suna tabbatarwa Allah abinda Ya tabbatarwa kanSa da shi na sunaye da siffofi ba tare da jirkitawa ko korewa ko kaifantawa ko kamantawa ba, kuma suna korewa Allah abinda Ya korewa kanSa, sunayin shiru daga abinda korewa ko tabbatarwa bai zo da shi ba, Allah - madaukakin sarki - ya ce: {Babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai yawan ji kuma Mai yawan gani}.
  • Kyautata zato ga Allah babu makawa daga aiki a tare da shi, al-Hasanul Basri ya ce: Lallai cewa mumini ya kyautata zato ga Ubangijinsa sai ya kyautata aiki, kuma lallai cewa fajiri ya munana zato ga Ubangijinsa sai ya munana aiki.
  • Al-Ƙurɗubi ya ce: An ce: Ma'anar "Zaton bawaNa gareNi" Zaton amsawa a yayin addu'a, da kuma zatan karɓa a yayin tuba, da zatan gafara a yayin istigfari, da zatan sakayya a yayin aikin ibada da sharuɗɗanta dan riƙo da gaskiyar alƙawarinsa, saboda haka yana kamata ga mutum ya yi ƙoƙari a tsayuwa da abinda ke kansa yana mai sakankancewa da cewa Allah Zai karɓe shi kuma Ya gafarta maSa; domin cewa shi ya yi alƙawari da hakan kuma Shi baYa saɓa alƙawari, idan ya ƙudirce ko ya yi zaton cewa Allah ba Zai karɓeta ba ko kuma cewa ba zata anfane shi ba to wannan shi ne yanke ƙauna daga rahamar Allah, kuma hakan yana daga manyan laifuka, wanda ya mutu akan hakan za'a wakilta shi zuwa abinda ya yi zato kamar yadda yake cikin sashin hanyoyin hadisin da aka anbata; "To bawaNa ya yi zato Na da abinda ya so", ya ce: Amma zatan gafara tare da nacewa akan sabo to hakan shi ne tsantsar jahilci da ruɗuwa.
  • Kwaɗaitarwa akan yawaita anbatan Allah a cikin ranka da harshenka gaba ɗaya, yana jin tsoron Allah a cikin ransa da zuciyarsa ya dinga tuna girmanSa da haƙƙinSa ya ƙaunace Shi ya girmamaShi ya so Shi ya kyautata masa zato ya tsarkake aiki, ya furta da harshe: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, babu wata dabara babu wani ƙarfi sai ga Allah.
  • Ibnu Abi Jamrah ya ce: Wanda ya anbace shi alhali shi yana mai jin tsoro zai amintar da shi, ko mai kewa zai ɗebe masa kewa.
  • Taki: (shi ne) faɗin dake tsakanin ƙaramin ɗan yatsa zuwa babban ɗan yatsa a yayin miƙe tafi. Zira'i kuwa: (shi ne) faɗin dake tsakanin gefen ɗan yatsa na tsakiya har zuwa ƙashin gwiwar hannu. Ba'i kuwa: (Shi ne) tsawon zira'i biyu na mutum da kuma damattsansa da faɗin ƙirjinsa; hakan (shi ne) gwargwadan zira'i huɗu.
Sharhi: العربية

أَخْبَرَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ اللهَ تعالى يقول: أنا عند ظن عبدي بي، فأُعَامِلُ عبدي على حسب ظَنِّهِ بي وذلك بالرجاء وتأميل العفو، وأَفْعَل به ما يَتَوَقَّعَه مني من خير أو غير ذلك؛ وأنا معه بالرحمة والتوفيق والهداية والرعاية والتأييد إذا ذكرني. فإنْ ذَكَرَني في نفسه مُنفردًا خاليًا بالتسبيح والتهليل أو غيرها؛ ذَكرتُه في نفسي. وإنْ ذَكَرَني في جماعة؛ ذكرتُه في جماعة أكثر منهم وأطيب. ومَن تَقَرّب إلى الله مقدار شِبْر زاده الله فتقرب إليه بذراع. وإن تقرب إليه مقدار ذراع تقرب إليه مقدار باع. وإن جاء إلى الله يمشي جاءه هَرولة. فالعبد إذا تقرب إلى ربه بطاعته والإقبال عليه، فإن الرب تعالى يَزِيده قُرْبًا إليه جزاءً مِن جنس عمله. فكلما كَمُلَتْ عبودية المؤمن لربه قَرُبَ إليه تعالى، فعطاء الله وثوابه أكثر من عمل العبد وكدحه، والحاصل أنّ ثواب الله راجِحٌ على العمل بطريق الكيف والكم. فالمؤمن يُحسِنُ الظن، ويعمل، ويسارع ويزداد حتى يلقى الله.

  • هذا الحديث مما يرويه النبي صلى الله عليه وسلم عن ربه، ويسمّى بالحديث القدسي أو الإلهي، وهو الذي لفظه ومعناه من الله، غير أنه ليست فيه خصائص القرآن التي امتاز بها عما سواه، من التعبد بتلاوته والطهارة له والتحدي والإعجاز وغير ذلك.
  • قال الآجُرِّي: إنّ أهل الحق يَصِفُون الله عز وجل بما وصف به نفسه عز وجل، وبما وصفه به رسوله صلى الله عليه وسلم، وبما وصفه به الصحابة رضي الله عنهم، وهذا مذهب العلماء ممن اتبع ولم يبتدع. انتهى. فأهل السنة يُثْبِتُون لله ما أثبته لنفسه من الأسماء والصفات من غير تحريف ولا تعطيل ولا تكييف ولا تمثيل، ويُنْفُون عن الله ما نفاه عن نفسه، ويَسْكُتُون عما لم يرد به نفي ولا إثبات، قال الله تعالى: (‌لَيْسَ ‌كَمِثْلِهِ شَيْءٌ وَهُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ).
  • إحسان الظن بالله لا بد معه من العمل، قال الحسن البصري: إنَّ المؤمن أَحْسَنَ الظنَّ بربه فأحسن العمل، وإنّ الفاجر أساء الظن بربه فأساء العمل.
  • قال القرطبي: قيل: معنى "ظن عبدي بي" ظن الإجابة عند الدعاء، وظن القبول عند التوبة، وظن المغفرة عند الاستغفار، وظن المجازاة عند فعل العبادة بشروطها تَمَسُّكًا بصادق وعْدِه، ولذلك ينبغي للمرء أن يَجْتَهِدَ في القيام بما عليه موقِنًا بأنَّ الله يقبله ويغفر له؛ لأنه وَعَدَ بذلك وهو لا يُخْلِف الميعاد، فإن اعتقد أو ظن أن الله لا يقبلها وأنها لا تنفعه فهذا هو اليأس من رحمة الله وهو من الكبائر، ومن مات على ذلك وُكِلَ إلى ما ظَنّ كما في بعض طرق الحديث المذكور " فليظن بي عبدي ما شاء"، قال: وأما ظن المغفرة مع الإصرار فذلك مَحْضُ الجهل والغِرّة.
  • الحث على الإكثار من ذكر الله في نفسك وبلسانك جميعًا، في نفسه وقلبه يخاف الله ويتذكَّر عظمته وحقه ويرجوه ويعظّمه ويحبه ويحسن به الظن ويخلص له العمل، وينطق باللسان: سبحان الله، والحمد لله، ولا إله إلا الله، والله أكبر، ولا حول ولا قوة إلا بالله.
  • قال ابن أبي جمرة: فمن ذَكَرَه وهو خائف آمَنَه، أو مُسْتَوْحِش آنَسَه.
  • الشِّبْر: مسافة ما بين طرف الخِنْصَر إلى طرف الإبهام عند مَدِّ الكَفّ، والذراع: مسافة ما بين طرف الأصبع الوسطى إلى عظم المرفق، والباع: طول ذِرَاعَي الإنسان وعَضُدَيه وعَرْضِ صدره؛ وذلك قدر أربعة أذرع.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari