Hadisai

Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa

Majiya: HadeethEnc.com, Hausa v1.25.0

Ingantacce neBukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Rubutun Larabci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «كُلُّ أُمَّتِي مُعَافًى إِلَّا المُجَاهِرِينَ، وَإِنَّ مِنَ المُجَاهَرَةِ أَنْ يَعْمَلَ الرَّجُلُ بِاللَّيْلِ عَمَلًا، ثُمَّ يُصْبِحَ وَقَدْ سَتَرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ، فَيَقُولَ: يَا فُلاَنُ، عَمِلْتُ البَارِحَةَ كَذَا وَكَذَا، وَقَدْ بَاتَ يَسْتُرُهُ رَبُّهُ، وَيُصْبِحُ يَكْشِفُ سِتْرَ اللَّهِ عَنْهُ».

Fassara

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Duk al'ummata an yafe musu sai masu bayyanarwa, kuma yana daga bayyanarwa mutum ya aikata wani aiki (mummuna) da daddare, sannan ya wayi gari Allah Ya rufa masa asiri, sai ya ce: Ya (ya falalarsa kansa) wane, jiya da daddare na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Uabangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa".

Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa musulmi mai laifi ana yi masa kwadayin afuwar Allah da gafararSa, sai mai bayyanar da sabo dan alfahari da rashin kunya, to ba ya cancantar afuwa; ta inda yake aikata laifi da daddare, sannan ya wayi gari alhali Allah Ya rufa masa asiri, sai ya zantar da waninsa da cewa shi ya aikata sabo kaza jiya, ya kwana Ubangijinsa Ya rufa masa asiri, shi kuma ya wayi gari yana tona asirin da Allah Ya rufa masa!!

Fa'idoji

  • Munin bayyanar da sabo bayan rufa asirin Allah - Madaukakin sarki - ya yi a gare shi .
  • A bayyanar da sabo akwai yayata alfasha tsakanin muminai.
  • Wanda Allah Ya rufa masa asiri a duniya Zai rufa masa asiri a lahira, wannan yana daga yalwar rahamar Allah - Madaukakin sarki - ga bayinSa.
  • Wanda aka jarraba da wani sabo to ya wajaba ya rufawa kansa asiri kuma ya tubarwa Allah.
  • Girman zunubin masu bayyanarwa wadanda suke nufin bayyanar da sabo, kuma suna barin afuwar Allah taba wuce su.
Sharhi: العربية

بَيَّنَ النبيُّ صلى الله عليه وسلم أنَّ المسلمَ المُذنبَ يُرجى له عفوُ الله ومغفرتُه، إلا المعلن بالمعصية تفاخُرًا ووقاحةً فلا يَستحقُّ العفو؛ حيث يَعملُ المعصيةَ بالليل، ثم يُصبِحُ وقد ستره الله، فيُحدِّث غَيرَه بأنه فَعَلَ المعصيةَ الفلانية أمس، وقد باتَ يَستُرُه ربُّه، ويُصبحُ يَكشِفُ سِتْرَ الله عليه!!

  • قُبح المجاهرة بالمعصية بعد سِتْرِ الله تعالى عليه.
  • في المجاهرة بالمعصية إشاعةُ الفاحشةِ بين المؤمنين.
  • مَن سَتَرَه الله في الدنيا سَتَرَه في الآخرة، وهذا من سعة رحمة الله تعالى بعباده.
  • مَن ابتُلي بمعصية عليه أن يَسْتُرَ على نفسِه وأن يَتوبَ إلى الله.
  • عِظم ذنب المجاهرين الذين يتقصدون إظهار المعاصي، ويُفوِّتون على أنفسهم المعافاة.

Maudu'ai

Ba da rahoton kuskure

Ƙari